Tsadar awon motocin gwanjo dake shiga Nijar daga kasashen turai wani abu ne da aka jima ana korafi akansa lamarin da ya sa jama’a suka fi maida hankali wajen sayen motocin da suka dade ana amfani da su don kaucewa biyan makudan kudaden awon Doune
Hakan ne mafari da gwamnatin kasar ta dauki matakin rangwame ga wadanda suka shigo da motocin da ba su fice shekaru 10 da soma zirga-zirga ba kamar yadda mataimakin babban darektan hukumar Douane colonel Abou Oubandaouaki ya bayyanawa a yayin taron manema labaran da ya kira.
Kungiyar masu sayarda motocin tourist a cewar kakakinta Alhaji Aminou Oumarou ta yaba da wannan mataki domin a cewarta abu ne da ko bayan habbaka harkokin kasuwanci zai bai gwamnatin damar samun kudaden shiga ta hanyar awo da biyan haraji.
Tsadar awon motocin gwanjo a Nijar wata matsala ce da ta sa masu fafitikar kare mahalli ke korafi akanta saboda a cewarsu abu ne da ke gurbata yanayi da muhalli sakamakon yadda jama’a ke karkata wajen sayen tsofafin motoci masu fitar da turiri maras iyaka a maimakon sayen motoci dake da lafiyar injin.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: