Shugaban Mohamed Bazoum yayin taron da ya kira a ranar juma’ar da ta gabata da nufin yiwa shugabanin al’ummar kasar bayani akan dalilan amincewa da shirin maido da sojojin Barkhane da na Takuba zuwa Nijer daga Mali, ya ce ya sallami wasu kwamandojojn kungiyar Boko haram daga gidan kaso wadanda kuma ya gana da su a fadarsa domin jan hankulansu akan munin abubuwan da suke aikatawa.
A cewar shugaban kungiyar Voix des sans Voix Alhaji Nassirou Saidou matakin na shugaban ya yi daidai.
Sai dai a nasa bangare shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta COADDH, Dambadji Son ALLAH ya nuna rashin dacewar jin wadanan kalamai daga bakin shugaban kasa saboda a cewarsa, magana ce ta sirrin kasa duk kuwa da cewa ya yi amanna da sulhu a matsayin hanyar warware kowane irin rikici.
Ministan bada horo da bunkasa sana’oin hannu Kassoum Maman Moctar na ganin alamun a na yiwa kalaman shugaban mumunar fahimta a wani lokacin da ya kamata dukkan ‘yan Nijer su hada kai don tunkarar kalubalen da ke gabanta inji shi.
Wannan shine karon farko da shugaban kasa ke tattara shugabanin rukunonin al’umma domin yin bayani akan batutuwan da suka shafi sha’anin tsaro tun bayan da kungiyoyin ta’addanci suka kaddamar da kai hare hare a kasar yau shekaru a kalla 7 kuma shine karon farko da ake shirin tuntubar majalisar dokokin kasa don neman izininta akan maganar girke sojan kasashen waje a Nijer duk da sukar da kungiyoyin fararen hula da jam’iyun hamayya suka sha yi a shekarun baya.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti :