Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa
Afirka

Kananan 'Yan Kasuwa Sun Bukaci A Janye Na'urar Tantance Kudin Harajin TVA


Kungiyar 'yan kasuwa
Kungiyar 'yan kasuwa

A jamhuriyar Nijer kananan ‘yan kasuwa sun bukaci hukumomin kasar su sake tunani a game da sabon tsarin biyan kudin harajin TVA da suka shimfida a farkon shekarar nan  ta 2022.

Wannan na nufin dole ne daga yanzu kowanne dan kasuwa ya yi amfani da wata na’ura wajen buga takardar saye da sayarwa ta yadda za a tantance zahirin kudin harajin da ya kamata ya zuba a ma’aikatar haraji, a tasu fahimtar biyan wannan haraji a yayin fiton kaya a ma’aikatar kwastam ita ce hanya mafi dacewa da yanayin kasar ta Nijer.

Rashin sanin kan digin na’urar da za a yi amfani da ita wajen tantance kudin harajin TVA da ya wajaba kowanne dan kasuwa ya biya, daidai da bayanan da ke rubuce a takardar saye da sayarwa wato facture certifiee ya sa kananan ‘yan kasuwa kiran mahukunta su sake duba wannan tsari da su ke yi wa kallon mara dacewa da yanayin kasar Nijer a bisa la’akari da jahilcin jama’a kamar yadda Malam Adamou Sama’ila mai magana da yawun kananan ‘yan kasuwa ya bayyana a wani taron manema labarai da suka kira .

A cewarsu biyan kudin harajin na TVA ta hanyar ma’aikatar kwastam ita ce hanya mafi a’ala da za ta basu damar sauke wannan nauyi.

Kafin ta soma zartar da wannan sabon tsari ma’aikatar haraji ta bayyana matakin a matsayin wata hanyar toshe kafar da wasu ke amfani da ita wajen kewayewa hanyoyin biyan haraji, to amma a cewar kananan ‘yan kasuwa suna da fargaba akan abinda zai biyo bayan dorewar wannan tsari.

A baya an sha kai ruwa rana a tsakanin kungiyoyin ‘yan kasuwa da hukumomin kula da sha’anin haraji dangane da wannan mataki da ke hangen kawo karshen satar haraji, sai dai tuni wasu ‘yan kasuwa suka fara fakewa da wannan sabon tsari wajen tsauwala farashin kayayaki musamman ababen masarufi.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:36 0:00

XS
SM
MD
LG