A Jamhuriyar Nijar dangi da abokan aikin wasu jami’an kamfanin BACOREX da ‘yan Boko Haram suka sace a farkon shekarar 2021 a dajin jihar Diffa sun bayyana damuwa akan halin rashin jin duriyar wadanan mutane.
Saboda haka ne suka kira taron manema labarai a birnin Yamai don tunatar da mahukuntan kolin kasar akan wannan batu.
A ranar 23 ga watan Janairun 2021 ne wasu ‘yan bindigar da ake hasashen mayakan Boko Haram ne suka yi awon gaba da Garba Amadou da wani mataimakinsa Youssef yayin da suka isa karkarar Gueskerou dake jihar Diffa domin gudanar da wani aikin gyaran layin sadarwa a karkashin kamfani BACOREX.
Wannan lamari ya faru ne jim kadan bayan da jami’an tsaron dake masu rakiya suka dakata a bakin ruwa.
Malan Ibrahim Hamadou wanda shi ne shugaban ma’aikatan kamfanin na BACOREX ya ce dama idan muna da abin yi a kudancin Gueskerou har ma baki dayan jihar Diffa ba ma fita sai da rakiyar jami’an tsaro.
Don haka kuma a wannan karon ma muna da rakiyar jami’an tsaro, sai dai an yi katari ruwan kogi ya gangaro a ranar. A ka’ida kuma jami’an tsaron dake wannan aiki ba sa shiga ruwa.
Wadanda suka yi garkuwa da wadanan ma’aikata sun tuntubi danginsu domin tattauna hanyoyin saki, sai dai ba su cimma daidaito ba in ji wani yayan Garba Amadou wato Aboubacar Ibrahim.
Ko da yake, ba su so" fada mana yawan kudaden da aka tambaye su a matsayin kudaden fansa ba." In ji shi.
Tun daga wancan lokaci komai ya tsaya cik ba wani bayani tsakanin ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da wadannan ma’aikata da danginsu na Yamai da iyalinsu dake Diffa ballantana su san halin da suke ciki.
Jihar Diffa mai makwaftaka da jihohin Yobe da Borno a Najeriya ta bangaren kudu, na da iyaka da kasar Chadi ta bangaren gabas, yankin ya fada cikin matsalar tsaro a shekarar 2015 kafin kura ta lafa a shekarar da ta gabata sakamakon matakan da hukumomin Nijar suka dauka.
Amma har yanzu ana ci gaba da fama da masu garkuwa da mutane da kuma barayin shanu.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: