Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta kaddamar da ayyukan rajistar tsofafin soja da nufin kafa wata rundunar musamman a ci gaba da karfafa matakan yaki da matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.
A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu bayan da kungiyar CEDEAO ta bayyana sunayen mutanen da zasu yi aikin shiga tsakani a kasashen Mali, Burkina Faso da Guinea inda sojoji suka yi juyin mulki.
A jamhuriyar Nijer hukumomin kiwon lafiyar al’umma sun gargadi maniyatan hajin bana dangane da muhimmancin mutunta ka’idodin kiwon lafiyar da hukumomin Saudiya suka shimfida da nufin dakile yaduwar cututtuka a lokacin hajin bana.
Sama da mutane 16,000 ne suka tsere daga matsugunansu a ‘yan watannin nan sakamakon tsanantar matsalolin tsaro a gundumar Torodi da ke jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso.
Hukumoin Jamhuriyar Nijar sun bukaci shugabanin matatar man SORAZ su gaggauta yin bitar adadin ma’aikata ‘yan Nijer da ‘yan kasashen waje a ci gaba da shirye shiryen mayarda al’amuran gudanarwar matatar a hannun jami’ai ‘yan Nijer.
Kotun ta ce girman laifin da Ousman ke zargin an yi masa bai kai matsayin da za a biya diyya ba, ko kuma wani abin da ke kama da haka saboda haka ta bai wa bangaren hukumomin Nijar gaskiya.
Kasashe 15 ne aka tantance domin shirya wannan zabe a bisa la’akkari da wasu muhimman sharudda.
A jamhuriyar Nijer, a yayin da direbobin motocin fisinja da na dakon kaya ke kokawa kan karancin man diesel a gidajen mai, kamfanin dillancin man fetur wato Sonodep na alakanta al’amarin da matsalar man da aka shiga a wasu kasashe makwabta sakamakon yakin Russia da Ukraine.
A Jamhuriyar Nijar an gudanar da bikin damkawa hukumomin kasar wata cibiyar da Majalisar Dinkin Duniya ta gina da hadin gwiwar wasu manyan kasashen duniya cikinsu har da Amurka domin karbar mutanen da suka tuba daga aika-aikar kungiyoyin ta’addancin da suka addabi jama’a a jihar Tilabery.
Bayan da ya je kasar Senegal, Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya isa birnin Yamai na Nijer inda ya gana da shugaba Mohamed Bazoum da mukarraban gwamnatinsa kafin ya ziyarci sojojin Jamus da ke aiyukan bada horo a karkashin rundunar hadin guiwar nahiyar Turai da ake kira La Gazelle.
A jamhuriyar Nijer wata kungiya mai zaman kanta ta kaddamar da ayyukan rajistar yara masu tawayar kwakwalwa da nufin tantance yawan irin wadanan bayun Allah dake bukatar a basu damar shiga makarantu tun suna kanana ta yadda watan-wata-rana zasu amfani kansu su kuma amfani al’umma.
Sai dai kawo yanzu, mutum daya tak ne aka gano a raye daga cikin wadannan dakaru.
A ranar 27 ga watan Nuwambar bara ne matasa suka datse mashigar garin Tera a wani lokacin da ayarin motocin sojan Barkhane ke shirin ratsa garin akan hanyarsu ta zuwa garin Gao, lamarin da ya sa Faransawan bude wuta akan wadanan mutane.
Laifukan da ake tuhumar sojojin sun hada da zargin yin fyade, batar kayan aiki sata da kuma arcewa daga aikin na soja.
A jamhuriyar Nijer masana sha’anin tsaro sun bayyana cewa matakin janyewa daga harkokin kungiyar G5 Sahel da gwamnatin mulkin sojan Mali ta dauka ba zai haifar wa kasar da mai ido ba, ganin irin muhimmiyar rawar da rundunar hadin gwiwar G5 Sahel ke takawa wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Bayanai sun yi nuni da cewa wasu mata kan taimaka wa ‘yan ta’adda wajen shirya aika-aikar da suke tafkawa.
Domin Kari