A wannan jawabi na tsawon mintoci kimanin 15 shugaban kasar ya fara da tunatar da al’ummar Nijer muhimmancin hadin kan ‘yan kasa. Bisa ga cewar shi , muddin aka zama tsintsiya madaurinki daya to kam za a iya tunkara kowace irin matsala .
Mohamed Bazoum ya ce wannan ne ya sa a washegarin darewarsa karagar mulki ya gana da shugabanin rukunonin al’umma don neman hadin kansu matakin da ya ce ya taimaka sosai wajen shimfida yanayin fahimtar dake tsakanin ‘yan kasa a yau.
A kan matsalar tsaro shugaban kasa ya bayyana gamsuwa da izinin da majalissar dokokin kasa ta bai wa bangaren zartarwa domin kulla huldar ayyukan soja da kasashe aminnai a matsayin wani yunkurin karfafa matakan yaki da ta’addanci ta hanyar musanyar bayanan dubarun yaki wanda ke daya daga cikin muhimman ayyukan da ke kunshe a tsarin manufofin gwamnati wato ‘Programme de la Renaissance Acte 3’. Ya na mai cewa ta’addanci da talauci na kan gaban abokan gabar Nijer da al’ummarta.
Mohamed Bazoum ya jaddada aniyar ci gaba da yaki da cin hanci da farautar mahandaman dukiyar jama’a kamar yadda ya sha alwashi a ranar da ya yi rantsuwar kama aiki, saboda a cewarsa banzantar da dukiyar kasa wata dabi’a ce da ta samu gindin zama a Nijer kamar yadda abin ya fito fili a rahoton da kotun kula da yadda aka kashe kudaden kasa wato ‘Cour des Comptes’ na baya bayan nan.
Shugaba Bazoum ya ce, yin watanda da dukiyar kasa babbar barazana ce ga ci gaban dimokaradiya haka kuma ‘yancin kai ba zai tabbata ba sai idan ana kula da dukiyar kasa kamar yadda ya dace. A nan shugaban ya ce ya umurci gwamnati ta dauki matakin zartar da shawarwarin da kotun ‘cour des comptes’ ta bayar don ganin an samu canjin tunani daga jami’an hukuma.
A fannin ilimi shugaba Mohamed Bazoum ya ce sakamakon jarabawar azuzuwan karshen makaratun sakandare matakin farko da na makarantun share fagen shiga jami’a na bana na nunin girman koma bayan da sha’anin ilimi ya shiga a Nijer saboda haka ya zama wajibi a kula.
Inganta ayyukan noma da kiwo ta hanyar amfani da hikimomin zamani wani abu ne da ya ce zai bai wa kulawar musamman ta yadda za a samu wadatar cimaka tare da bunkasa kamfanoni da masana’antu.
Mohamed Bazoum ya gargadi kasashe masu karfin tattalin arziki a game da nauyin da ya rataya a wuyansu dangane da illlolin canjin yanayi a kasashe masu tasowa irinsu Nijer.
A bana jihar Tilabery ce ke karbar bakuncin shagulgulan ranar samun ‘yancin kan Nijer saboda haka tun a yammacin jiya shugaban kasa ke bakuntar al’ummar wannan jiha don jagorancin ayyukan dashen itace a wunin wannan Laraba.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma cikin sauti: