Domin raya wannan rana ta cika shekaru 62 da kafa rundunar sojojin Nijer, an gudanar da wani biki na musamman a barikin sojoji Camp Gamo dake birnin Yamai.
Haka kuma wannan ya kasance wani lokacin bitar aiyukan da dakarun tsaron kasar suka gudanar a tsawon shekaru 62, da nufin kara jan damara musamman a wannan lokaci na lalacewar sha’anin tsaro da ya addabi yankin Afirka ta yamma.
Bayan da ya yi tunatarwa akan dokar da ta kafa wannan runduna da kuma irin jan aikin da ta gudanar a tsawon shekaru 62 ministan tsaron kasa, Alkassoum Indatou, ya bayyana shirin da hukumomi suka sa gaba da nufin tunkarar kalubalen da ke neman zama ruwan dare a kasashen yammacin Afrika.
Ya ce a washegarin kafuwar rundunar ta fara aiki ne da dakaru 818 kawai, cikin su hafsoshi 6 da kananan hafsoshi 36 da kuratan sojoji 776, yayin da a yau ake da sojoji dubu 33, kuma a cewar sa gwamnatin Nijer na hangen kara yawan wadanan asakarawa zuwa dubu 50 kafin nan da shekarar 2025 watakila ma su kai dubu 100 zuwa shekarar 2030.
Dukkan manyan kwamandojin soja sun hallara wurin wannan buki na karrama dakarun tsaron, haka kuma an gayyato jama’a a wannan haduwa da a dai bangare ta kasance wata dama ta gudanar da aiyukan dashen bishiyoyi.
Ganin yadda sojojin Nijer ke tsayin daka a kowace rana don tabbatar da tsaro a kasar da akasarin makwaftanta ke fama da kungiyoyin ta’addanci da na ‘yan bindiga, ya sa jami’an fafitika da suka halarci bukin ranar ta rundunar sojoji irinsu Issa Garba na Tournons La Page jan hankula akan maganar kyautata yanayin rayuwar illahirin jami’an tsaro.
A sauran jihohi ma an yi hidimomin tunawa da ranar zagayowar kafuwar rundunar ta Forces Armees Nigerienne wadda ke ci gaba da samun jinjina saboda nasarorin da dakarunta ke samu.
Domin Karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.