Ranar Lahdi 19 ga watan Yuni kasashen duniya ke bikin tunawa da ranar yaki da cutar amosanin jini wacce ke daya daga cikin cututtukan da suka fi wahalar da jama’a a kasashe masu tasowa sakamakon karancin asibitoci da tsadar magunguna.
Yanayin tsaron da aka shiga akan iyakar Burkina Faso da jamhuriyar Nijar ya sa wasu kamfanonin jigila dakatar da zirga-zirga tsakanin birnin Yamai da Ouagadougou da nufin kaucewa fadawa tarkon ‘yan bindiga da suka addabi wannan yanki.
A jamhuriyar Nijar yau aka yi bukin yaye wasu sabbin hafsoshin da suka shafe watanni 8 suna karantar dubarun yaki a matsayin wani bangare na yunkurin da hukumomin kasar suka sa gaba wajen neman hanyoyin tunkarar kalubalen tsaron da ake fama da su a ‘yan shekarun nan.
Ma’aikatar tsaron jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar rasuwar wasu jami’an tsaron kasar sannan wasu kuma suka samu rauni a yayin dauki ba dadin da ya hada su da ‘yan ta’adda a kauyen Waraou na jihar Tilabery a jiya talata 14 ga watan Yuni.
Wani rahoton hukumar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) mai kula da kaurar jama’a wato IOM ya gano cewa galibin mutanen da ke shiga hannun masu safarar mutane akan hanyoyin dake ratsa Jamhuriyar Nijer zuwa kasashen Larabawa da na yammacin duniya mata ne da ‘yan mata suke shiga tashin hankali.
Wasu hare hare da aka kai kwanan nan a kauyen Seytenga na kasar Burkina Faso sun yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da tilasta wa mutane kusan 3,000 tserewa daga matsugunansu, lamarin da ya sa masu nazari akan sha’anin tsaro suka fara jan hankalin gwamnatocin kasashen yankin.
A yayin da ranar Lahadi 12 ga watan Yuni ake bikin ranar yaki da bautar da yara, kungiyoyin kare hakkokin yara a jamhuriyar Nijar sun bayyana damuwa a game da yadda ake ci gaba da aikata wannan haramtacciyar dabi’a a wasu yankunan kasar.
A ci gaba da neman hanyoyin farfado da sha’anin ilimi ke fuskanta a jamhuriyar Nijer, gwamnatin kasar ta shigar da wasu malaman sakandare ‘yan kwantaragi sama da 2000 a sahun malaman dindindin ba tare da yin wata jarabawa ba.
A jamhuriyar Nijer kungiyoyin addinin islama sun gargadi hukumomin kasar da ‘yan majalisar dokoki su janye wasu dokokin da suke shirin shimfidawa a kasar da nufin kare hakkin mata da yara kanana, matakan da suka ce sun ci karau da addini.
Sai dai kakakin jam’iyar PNDS mai mulki, Assoumana Mahamadou, ya yi watsi da wannan zargi hasali ma a cewarsa masu wannan ikirari mutane da ke da wata manufa ta boye.
Mutane sama da 500 wadanda suka hada da mata da yara har da tsofaffi ne jirgin Max Air ya sauke a filin jirigin saman Diori Hamani da misalin karfe 3 na ranar wannan Laraba 8 ga watan Yuni,
Gwamnatin Jamhuriyar Nijer ta kaddamar da ayyukan rajistar tsofafin soja da nufin kafa wata rundunar musamman a ci gaba da karfafa matakan yaki da matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.
A Jamhuriyar Nijar wasu ‘yan kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu bayan da kungiyar CEDEAO ta bayyana sunayen mutanen da zasu yi aikin shiga tsakani a kasashen Mali, Burkina Faso da Guinea inda sojoji suka yi juyin mulki.
A jamhuriyar Nijer hukumomin kiwon lafiyar al’umma sun gargadi maniyatan hajin bana dangane da muhimmancin mutunta ka’idodin kiwon lafiyar da hukumomin Saudiya suka shimfida da nufin dakile yaduwar cututtuka a lokacin hajin bana.
Sama da mutane 16,000 ne suka tsere daga matsugunansu a ‘yan watannin nan sakamakon tsanantar matsalolin tsaro a gundumar Torodi da ke jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso.
Hukumoin Jamhuriyar Nijar sun bukaci shugabanin matatar man SORAZ su gaggauta yin bitar adadin ma’aikata ‘yan Nijer da ‘yan kasashen waje a ci gaba da shirye shiryen mayarda al’amuran gudanarwar matatar a hannun jami’ai ‘yan Nijer.
Kotun ta ce girman laifin da Ousman ke zargin an yi masa bai kai matsayin da za a biya diyya ba, ko kuma wani abin da ke kama da haka saboda haka ta bai wa bangaren hukumomin Nijar gaskiya.
Kasashe 15 ne aka tantance domin shirya wannan zabe a bisa la’akkari da wasu muhimman sharudda.
Domin Kari