NIAMEY, NIGER. - Ministan harkokin wajen jamhuriyar Nijer Hassoumi Massaoudou, da ke bayyana matsayin gwamnatin kasar dangane da yakin da Rasha ke kafsawa da Ukraine, ya nuna a fili karara rashin dacewar wannan yaki da ke zubar da kimar nahiyar Turai a game da maganar mutunta ‘yancin kasa da kasa.
Ya ce tun bayan kammala yakin duniya na biyu an yi zaton ba za a sake fuskantar barkewar yaki a Turai ba amma kuma yau an wayi gari nahiyar ta fada cikin yanayin yaki wanda shi ne mafi muni a tarihin duniya, ganin yadda daga cikin manyan kasashen duniya wata ta mamaye makwabciyarta, abinda ya ce suke ganin ya saba wa dokokin kasa da kasa ya kuma saba wa dokokin Majalisar Dinkin Duniya.
"Dokokin kasa da kasa ne ke bai wa kasashe irin namu damar cin gashin kansu domin ba mu da karfi idan haka siddan za a wayi gari saboda ji da kai wata kasa ta mamaye makwabciyarta, ba maganar ‘yanci ko kuma dokokin kasa da kasa, shi ya sa muke bin sahun kasashen da ke Allah wadai da wannan mamaya irin ta zamanin jahiliya," a cewar Massaoudou.
Ya kara da cewa hakan ne ma ya sa tun a tashin farko suka goyi bayan kudirin Majalisar Dinkin Duniya a game da rashin cancantar wannan yaki.
Ministar harkokin wajen Faransa Catherine Colonna ta yaba da matsayin na hukumomin Nijer dangane da yakin na Rasha a Ukraine. Ta ce tsarin tafiyar siyasar duniya ya shiga cikin halin kangin da bai taba fuskanta ba a sakamakon yakin da Russia ta kaddamar a Ukraine.
"Matsayin Nijer abu ne da ya je daidai da matsayin kasashen duniya saboda abu ne da ke taba ‘yancin rayuwa kamar yadda dokokin kasa da kasa suka shata. Mu ma muna tur da kashe kashen, wanda Rasha ke da alhakinsa a yakin da ta kaddamar," a cewar Colonna.
Wadannan ministoci sun bayyana matsayin kasashen nasu ne a yayin ziyarar da ministar harkokin wajen Faransa da abokin aikinta na tsaro suka gudanar a ranakun Alhamis da Laraba a Nijer dabra da tattaunawar da suka yi da takwarorinsu a game da tsarin daftarin da dakarun kasashen biyu zasu yi amfani da shi a fagen daga bayan kaurar sojojin Barkhane daga Mali zuwa Nijar.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: