‘Yan Najeriya na ci gaba da maida martani game da cece-kucen da ake yi game wasu marayun kudade kimanin Naira Miliyan 250 da Hukumar EFCC ta sake kamawa sakamakon kwarmaton da masu fallasa bayanai suka yi a birnin Ikko, yanzu haka masana na ganin akwai abin dubawa.
Amurka na kira ga kasashen yankuna daban-daban ciki har da Rasha da Pakistan, da kar su goyi bayan 'yan kungiyar Taliban a kokarinsu na cigaba da tsawaita dadadden yakin nan na Afghanistan.
Wata kotun Masar ta sallami wata ba-Amurkiya 'yar asalin Masar tare da wasu mutane 7, bayan kasancewa a daure na kusan tsawon shekaru uku saboda zargin safarar mutane ta wajen amfani da wata kungiyarta mai da'awar taimakon yaran da ke kan titin Alkhahira.
Mataimakin Shugaban Kasar Amurka Mike Pence ya jaddada karfin kawancen Amurka da Koriya Ta Kudu 'yan sa'o'i bayan cikas na baya-bayan nan da Koriya Ta Arewa ta samu a gwajegwajen makamai masu linzamai da ta ke yi.
Jam'iyya mai mulkin Turkiyya ta yi ikirarin yin nasara a zaben raba gardama na kara ma Shugaba Tayyib Erdowan dinbin iko, bisa ga sanarwar da hukumomi su ka yi da daren jiya Lahadi.
Cibiyar addinin musulunci ta Najeriya mai suna Ummatul Islam ta gudanar da taron ta na shekara shekara, mai taken ‘aikin gona a zaman mafita ga matsalar tattalin arziki a Najeriya'.
Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa ambaliyar ruwa ta yi mummunar barna a wasu gonakin noman rani, lamarin da ya jawo asarar amfanin gona na dubban Nairori.
Gwamnatin tarayya da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross da kuma jami’ar Amurka a Najeriya, zasu fito da wani shirin magance matsalolin ‘yan gudun hijira a arewa maso gabas da zai samar da wata kafa don aiki tare da ‘yan gudun hijiran wajen shawo kan matsalolinsu na yau da kullum.
Mahukunta a kasar Libya sunce wani jirgin ruwa dake dauke da bakin haure ya nutse a cikin tekun Bahar-Rum jiya alhamis kuma yayi dalilin mutuwar yan kasar ta Libya har su 97.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, ya ‘kara tabbatar da alwashin gwamnatinsa na cewa tana daukar duk matakan da suka kamata wadanda suka hada da na sulhu da kuma na karfin bindiga don tabbatar da cewa an sako ‘yan matan Chibok da duk wasu ‘yan Najeriya da ke hannun ‘yan Boko Haram.
Amurka ta amince za ta sayarwa Najeriya manyan jiragen yakin nan samfurin A29 Super Tucano guda 12, don gamawa da sauran burbushin Boko Haram.
A jiya laraba ne kasar Rasha ta sake hawa kujerar naki domin kare shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad, daga sukar da yake sha daga kasashen duniya game da harin makami mai guba.
Shugaban Somalia ya lashi takobin ganin sai yaga karshen kungiyar ‘yan ta’addar nan na al-shabab, a cikin shekaru biyu daga yanzu, kana kuma ya bukaci shugabannin da suzo domin a tattauna dasu.
Koriya ta Arewa ta samar da wata na’ura a cikin hanyar ta ta karkashin kasa inda take gwada makamin ta na Nukiliya.
Asusun tallafawa ‘kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce anyi amfani da ‘kananan yara har 117 wajen kai harin kunar bakin wake a kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi cikin shekarar 2014 kawai.
Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Dakta Goodluck Jonathan ya musunta zargin da aka yi masa na cewa ya karbi wasu makudan kudade lokacin da suka sayarwa da kamfanin Shell da Eni wata rijiyar Mai a yankin Niger-Delta.
Daruruwan ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya sun gudanar da wani gangami a Jalingo, domin nemawa kananan hukumomi ‘yancin cin gashin kai.
Shugaba Donald Trump ya amincewa Montenegro ta shiga kungiyar NATO jiya Talata, wanda wani cigaba ne ga wannan karamar kasar ta yankin balti da ke fafatukar ganin an amince da kokarinta na shiga kungiyar ta NATO.
Kungiyar da ke sa ido kan cin hanci da rashawa a Duniya ta Global Witness ta ce ta gano wata babbar tabargazar cin hanci da rashawa da ta shafi bangaren Mai, wadda Kamfanin Man Shell da Najeriya ke da hannu ciki dumu-dumu.
A karo na biyu cikin watanni 6 an kama babban jagoran 'yan adawa a kasar Zambia mai yawan magana kuma gabansa gadi, a cewar mai magana da yawun jam'iyyarsu a bayaninsa ga Muryar Amurka jiya Talata.
Domin Kari