Shugaba Mohammed Abdullahi Mohammed wanda ake wa lakabi da Farmajo yana Magana a jiya, wurin bikin cika shekaru 57 na samar da gidauniyar sojojin kasar, bikin wanda aka gudanar a cikin harabar ma’aikatar tsaron kasar dake Magadishu.
‘’Yace muna baiwa mutanen kasar nan tabbacin cewa cikin shekaru daga yanzu sai mun kawo karshen kungiyar Al-shabab duk inda suke cikin kasa’’.
Yace kungiyar ta kwashe shekaru da dama tana aiwatar da taaddanci amma kuma ta gaza karbe ragamar gwamnatin kasar.
Shugaba Mohammed yace don haka yana kira ga shugabannin kungiyar da su fito fili domin a yi sulhu dasu, idan kuma sun kiya to za a zakulo duk inda suke a cikin kasa.
Yace a shirye gwamnati take ta tattauna dasu.
‘’Yace kun kai shekaru 10 yau kuna fada da gwwamnati amma kun gaza karbe ragamar mulkin kasar wanda keda da goyon bayan kasashen duniya, don haka ku fito daga maboyar ku domin a tattauna amma idan kunki to zamu biku inda kuka boye domin fito daku, ba zaku iya ture gwamnati ba sai dai kawai ku dushe hasashen ‘yan kasa.
Facebook Forum