Ana sa ran zata yi gwajin makamin nukiliya ranar Asabar ko kuma kafin wannan ranar, kamar yadda wata majiya gwamnatin Amurka dama wasu suka labarta.
Ba za muce kome ba, amma muna nan mun zura ido, kamar yadda wani jami’in hukumar tsaro ya shaida wa Muryar Amurka.
A ranar Asabar din dai Koriya ta Arewa ta yi bikin tunawa da shugaban ta da ya kafa ta.
Wannan na’urar gwajin dai an shirya ta tsaf wanda kuma shine irin sa na 6 kamar yadda Joseph Bermudez Jr da Jack Liu ke cewa.
Wannan gwajin dai ba shakka tamkar ci gaba ne da harzuka kasar Koriya ta kudu inji mai Magana da yawun Babban hafsan sojan kasar Roh-Jae-Chun sailin da yake tattaunawa da manema labarai a Seoul yau da safe lokacin kasar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a taron manema labarai jiya sailin da suke tare da sakataren kungiyar NATO wanda ya kawo masa Ziyara, wato Jen Stoltenberg, cewa yayi Magana da shugaba China Xi-Jinping domin ya taimaka yayi Magana da Koriya ta Arewan, amma idan hakan bata samu ba, to mu zamu dauki matakin da muke jin ya dace.
Facebook Forum