A jiya Laraba ma’aikatar Shari’a ta Amurka, ta ce ta nada tsohon shugaban hukumar binciken laifuka ta FBI, Robert Mueller, a matsayin mai bincike na musamman kan yunkurin gwamnatin Rasha na yin katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na shekarar da ta gabata, da kuma wasu batutuwa da suka shafi Rasha.