Shugaban hukumar Alhaji Maikanti Kacalla Baru ne ya bayyana hakan a wata ziraya da ya kai jihar Borno, don jajantawa al’ummar jihar game da halin da suka shiga da kuma tayin taimako ga gwamnatin jihar.
Kusan shekaru 30 kenan ake ta batun tono Man Fetur a yankin na tafkin Chadi, sai dai Alhaji Maikanti ya ce yanzu lokaci yayi da zasu tabbatar da cewa an ci gaba da hakko ma’adanan Man Fetur da kuma iskar gas a yankin. Ya ce yanzu haka ma sun ci gaba da tono Mai a yankin Niger-Delta, sakamakon zaman lafiya da aka samu a bangaren.
‘Daya daga cikin manyan daraktocin hukumar NNPC, Injiniya Sa’idu Mohammad, ya ziyarci fadar gwamnatin jihar da kuma fadar mai martaba Shehun Borno, wanda dukkanninsu ya tabbatar musu da cewa za a ci gaba da hakko ma’adanan Man Fetur da Iskar Gas nan ba tare da bata lokaci ba.
Gwamnan jihar Borno, yace zasu yi murna da duk wani taimako da hukumar za ta yiwa jihar, amma basa bukatar kudi daga hukumar sai dai duk wani taimako da hukumar za ta yi ya kasance irin na gina ajujuwan karatu da ‘dakunan shan magani da kuma kayayyakin gine-gine.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum