Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Gargadi Kasashen Duniya Kan Koriya Ta Arewa


Taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan Koriya ta Arewa.
Taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan Koriya ta Arewa.

A jiya Talata ne jakadiyar Amurka a MDD Nikki Haley ta fadawa kasashen duniya cewa, dole ne kasashe su hada kai wajen yunkurin hana kasar da Koriya ta Arewa mallakar makaman Nukiya, tana mai yi musu gargadin zasu iya fuskantar wasu takunkumi idan har suka taimakawa Koriyar wajen samun nasarar shirin ta na Nukiliya.

Haley, ta yi wannan furucin ne kafin a kamalla taron kwamitin sulhun MDD , wanda Amurka da Japan da Koriya ta Kudu suka bukaci ayi, don tattaunawa kan gwaje-gwajen makamai masu linzami na Koriya Ta Arewa na baya-bayan nan.

Da take magana da manema labarai Haley ta ce “Cikin biyu ne, ko kana goyon bayan Koriya ta Arewa ko kana goyon bayan mu, saboda wannan shine zabin kawai.”

Da take magana kan tabbatar da wasu takunkumi ga kasashen duniya, ta ‘kara da gargadin cewa: “Amurka tana lura da kasashen da ke taimakawa Koriya ta Arewa, kuma za’a saka musu takunkumi, saboda idan ‘kasa na taimakawa Koriya ta Arewa, to bata goyon bayan sauran kasashen duniya.

Mambobin kwamitin dai sun gana jiya Talata, biyo bayan gwaje-gwajen makaman da Koriya ta Arewa ta yi wanda suka hada da daga mai matsakaicin zango, zuwa mai dogon zango wanda yayi tsawon tafiyar kilomita 800 kafin ya fada cikin kogin Japan.

Wannan shine gwajin makamai na biyu da Koriya ta Arewa ta yi a ‘yan makonnin nan, wanda kuma ya zo kwanaki hudu bayan da sabon shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae ya dare mulki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG