Mai magana da yauwan shugaban Mohammadu Buhari, Femi Adesina, bai bayar da wani cikakken bayani ba, amma ya ce Sojojin Najeriya ne suka samo yarinyar kuma suka ‘dauketa zuwa babban birnin tarayya Abuja.
Kubutar ‘dalibar dai yazo ne makonni biyu bayan da kungiyar Boko Haram ta yi wa gwamnatin Najeriya musayar ‘yan mata 82 ita kuma ta saki fursuna. Cikin ‘yan kwanaki masu zuwa ake kyautata tsammanin ‘yan matan zasu sake haduwa da iyayensu.
Kungiyar Boko Haram ta sace ‘dalibai ‘yan mata 276 a makarantar sakandare ta Chibok, a shekarar 2014, wanda ya tayar da hankulan Miliyoyin mutane a fadin Duniya.
An saki ‘yan mata 21 a watan Oktoba, yayin da wasunsu da dama suka kubuta ‘daya bayan ‘daya.
Amma dai har yanzu ‘yan mata sama da 100 suna hannun Boko haram.
Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane a shekaru 8 da ta kwashe tana tayar da hankali a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Facebook Forum