Wata kungiyar bada shawara akan yada sahihan labaru, mai suna Community Information Technology and Development a turance ta ce jita jita ce makamashin rura fitina a tsakanin al’ummar Nigeria
Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya ta nisanta kanta daga kalaman da wani ya yi da cewa kashe-kashen kwanannan a Filato ramuwar gayya ne Fulani suka yi.
Jam’iyya mai mulki a Najeriya APC ta kammala babban taron da ta yi a Abuja inda ta sake zabar sabbin shugabaniin da zasu gudanar da al’amuran jam’iyyar.
Jam’iyyar APC mai mulki ta gudanar da babban taronta a Dandalin Eagle dake babban birnin Abuja.
Tsohon kakakin jam'iyyar APC Timi Frank ya yabawa gwamnati Buhari da karrama Marigayi Moshood Abiola da aka dauka shi ya lashe zaben 1993. Sai dai ya soki gwamnatin da cewa tana murkushe turakun dimokradiyya da watsi da umarnin kotu.
Ana ci gaba da yin mahawara kan yadda hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta ke mikawa wadanda take tuhuma kwali ko allo dake rubuce da laifi maimakon tuhuma da ake musu, kuma su daga a dauki hotonsu.
Ana bukatar kwana cikin shirin bayan hasashen ruwa mai karfin da ka iya haddasa ambaliyar ruwa da kuma tsaiko, inda ruwan zai dauke na wani lokaci yayin da amfanin gona ya fara yi.
Masana harkokin tsaro a Najeriya na ganin ‘karin daukar jami’an ‘Yan Sanda aiki shine masalahar tsaro a kasar.
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce a shirye ya ke a bincike shi kan kashe dala biliyan 16 wajen samar da wutar lantarki da Shugaba Buhari ya ce ba a gani a kasa ba.
Kwamitin raya yankin arewa maso gabas na bukatar Naira Tiriliyan biyu cikin shekaru goma, don aikin raya yankin arewa maso gabas da hakan zai baiwa dukkan wadanda suka rasa muhallansu damar komawa garuruwansu na asali.
Kungiyar da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya kafa don kawar da shugaba Buhari daga mulki ta shiga jam’iyyar adawa ta ADC, da nanata kudirin kawo sabbin jini a harkokin siyasa.
Babban bankin Najeriya CBN da na kasar China sun shiga yarjejeniyar musayar kudin kasashen biyu, don saukaka huldar kasuwanci ba tare da neman dalar Amurka ba.
Gwamnatin Najeriya ta hana shigowa ko sarrafa duk wani ruwan maganin hana tari dake ‘dauke da sinadarin Codeine.
Gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da karar tuhumar shugaban kungiyar Shi’a na kasa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da laifin kisan kai.
Kalubablen rashin guraban aiki da karancin albashi shi ne ke haddasa likitoci da jami’an jinya na ungozoma da suka yi karatu a Afirka, su fice zuwa kasashen ketare, musamman na turai domin yin aiki.
Yayin da zaben shekarar 2019 ke karatowa hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC na cewa ta dauki matakan hana duk wani magudi.
Domin Kari