Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daminar Bana: Akwai Yiwuwar Ambaliyar Ruwa A Najeriya


Wata ambaliyar ruwa a Somalia
Wata ambaliyar ruwa a Somalia

Ana bukatar kwana cikin shirin bayan hasashen ruwa mai karfin da ka iya haddasa ambaliyar ruwa da kuma tsaiko, inda ruwan zai dauke na wani lokaci yayin da amfanin gona ya fara yi.

Shugaban hukumar nazarin hasashen yanayi a Najeriya wato NIMET, Farfesa Sani Abubakar Mashi, ya ce za a samu wadatar ruwan sama amma akwai kalubalen da ya kamata 'yan Najeriya su yi la'akkari da shi.

"Akwai matsaloli irinsu tsawa, da irin ruwan nan da ya ke zuwa da yawa a cikin takaitaccen lokaci wanda ke sa a samu matsalolin ambaliya ruwa."

Mashi ya yi wannan bayanin ne a wajen taron da hukumar ta yi don wayar da kan manoma da sauran jama'a kan yadda daminar bana za ta kasance bisa binciken kimiyya ba yanayi na shaci-fadi-ba.

A cewar shugaban, duk da cewa za a samu ruwa kamar yadda aka saba a Najeriya, amma akwai daidaikun wuraren da za a samu ruwa fiye da yadda aka saba samu wanda zai haddasa matsalar ambaliyar ruwa. Saboda haka ya kamata a kwana cikin shiri.

Sannan ya bayyana cewa ana sa ran samun matsalolin da ake samu da farko da kuma karshen damina kamar yawan iska mai haddasa barna inda za ka itatuwa sun fadi, gidaje sun rushe, da dai sauransu.

Abu na karshe da ake sa ran zai faru a cewarsa shi ne, tsaiko da ake samu inda za a ga an fara ruwa, sai kuma ya dauke yayin da amfanin gona ya fara yi, wato 'dry spell' a turance. Wanda ya ce zai banbanta, inda a wani wuri zai kai kwanaki goma wani wuri kuma kwanaki goma sha takwas.

Ministan zirga-zirgan jirage na Najeriya, Hadi Sirika ya ja hankalin manoma da suka rika tuntubar masana yanayi don sanin lokacin shuka da kuma yiwuwar tsawo ko karancin ruwan damina a shekarar.

"Ranar da aka ce za a fara ruwa a Funtua, ranar aka fara, ranar da aka ce ruwan zai tsaya, ranar ya tsaya. Saboda haka manomi, zai iya sanin yawan ruwan da za a yi a garinsu. To kaga ba zai je yayi abinda ake kira bisne ba a da,wato in an ji kamshin damina ko ruwan farko, sai mutane su je su yi bisne." inji shi

Ya kuma yi kira ga manoma, cewa kimiyya da fasaha wata rahama ce daga Allah tunda shi ya bada ilimin da har aka kirkiro da jiragen sama da za a iya tafiyar kwanaki cikin sa'o'i, saboda haka ya kamata a yarda da wannan ilimin da ya bada damar gane lokacin da ruwa zai sauka da lokacin da zai dauke.

Saurari cikakken rohoton Nasiru El-hikaya

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG