Ministan lafiya na Najeriya Isaac Adewole, shine ya sanar da matakin gwamnatin Najeriya na hana shiga ko sarrafa duk wani ruwan maganin tari dake dauke da sinadarin Codeine, da wasu ke amfani da shi don samun maye.
Adewole ya ce za a tabbatar da daukar wannan matakin ta hada hannu da duk jami’an yaki da fataucin miyagun kwayoyi da cibiyoyin wayarwa don hana amfani da sinadarin Codeine.
Haka kuma za a bi duk dakunan sayar da magani don tabbatar da daina amfani da maganin, mai gusar da hankali idan aka yi amfani da shi ta hanyar da bata dace ba. Maimakon sinadarin Codeine ma’aikatar lafiya ta ce sai a rinka amfani da sinadarin “DEXTROMETHORPHAN" wanda bashi da illa ko tsanani, kuma yana samar da waraka ga mura ko tari.
Ministan Matasa da Wasanni na Najeriya Solomon Dalung, ya nuna damuwa kan ta’azzarar shan kwalabe masu kawar da hankali. Inda ya ce lamarin ya shafi al’umma gaba daya tun da har mata ma na amfani da miyagun kwayoyi.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum