A Najeriya ba sabon abu bane batun yadda tsoffin gwamnoni da ke Majalisar Dattawa ko ke rike da mukamin minista ke ci gaba da karbar fansho da alawus na aikin gwamnan, da alawus na lafiya, da walwala daga jihohinsu.
Shugabar wata kungiya mai da’awar samar da shugabanci na gari, Victoria Ose Udo, ita ce ta sake tado da batun a wani taro a Kaduna, da ke nuna cewa akalla tsoffin gwamnoni 21 da mataimakansu na ci gaba da karbar wasu kudaden alhali ‘yan fansho na zaman jira a biyasu na su hakkin ba.
Shugaban kungiyar kwadago ta NLC Kwamarad Ayuba Wabba, ya ce ba rashin kudi bane yake sa gwamnatoci basa biyan ma’aikata hakkokinsu ba, face rashin ganin ‘kima da amfanin ma’aikatan yasa ba a biyansu.
Ya zuwa yanzu dai akwai jihohi 15 a fadin Najeriya da basa biyan ma’aikatansu albashi yadda ya kamata, duk kuwa da kudaden da aka mayar musu na Paris Club.
A wannan makon ne tsohon shugaban Najeriya na soja, janar Yakubu Gawon, ya bukaci a karawa ma’aikata albashi, don hakan ya taimaka wajen hana cin hanci da daidaito tsakanin ‘yan siyasa da ma’aikatan.
Zai yi wahala a soke wannan gajiya da tsoffin gwamnoni da mataimakansu ke samu domin majalisun dokoki ne ke amincewa da biyan kudaden.
Domin karin bayani, saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.
Facebook Forum