Ambaliyar ruwa mai tsanani da ta shafi musamman wasu jihohin arewa maso yammacin Najeriya wansa shi ne mafi yawan jama'a, ya kawo fargabar yiwuwar a samu karancin abinci, saboda yanda ruwan ya shafe gonaki ya maida su tamkar kananan koguna.
Shugabar hukumar bunkasa zuba jari a Najeriya (NIPC) Yewande Sadiku, ta ba da tabbacin aiki da hukumar kasuwanci ta jiragen ruwa wajen samun rage haraji don kara janyo hankalin masu zuba jari su ci gaba da shigowa Najeriya.
Majalisar Limaman birnin Abuja ta gudanar da gagarumin taro don karfafa Limamai gwiwa su ci gaba da tsayawa kan gaskiya tare da gujewa marawa wani bangaren siyasa baya.
Duk da matsin tattalin arziki da yawan sanyin guiwa da ‘yan Najeriya ke nunawa, hakan bai hana gwamnatin da jama’a daukar cika shekaru 60 da samun ‘yanci abu mai muhimmanci ba.
Hukumar zaben Najeriya ta ce gayyaci kamfanoni don kera na'urar da ta dace da nufin komawa kada kuri'a nan gaba ta hanyar na'ura mai kwakwalwa.
Kungiyar Kwadagon Najeriya ta NLC da gamayyar kungiyoyin kwadago ta TUC, sun janye yajin aikin gama-gari da suka shirya shiga yau Litinin, 28 ga watan Satumban shekarar 2020, akan karin farashin man fetur da wutar lantarki.
An shiga jajiberin ranar da kungiyar kwadagon Najeriya NLC za ta auka yajin aiki da ma zanga-zanga don matsawa gwamnati lamba ta janye karin farashin fetur da lantarki da ta yi da tuni hakan ya fara tasiri a kan farashin kayan masarufi.
Hukumar kula da rayuwar dabbobi ta Majalisar Dinkin Duniya da masu kare hakkin dabbobi na Afirka, sun nuna damuwa ga yadda Jakuna ke matukar raguwa a duniya, saboda kashe su da a ke yi don samun nama da kuma amfani da fatar su wajen magani a kasar China.
Kungiyar tattaunawa tsakanin Musulmi da Kirista ta “Interfaith Dialog for Peace” ta ce kauce wa kiyayyar addini da kabilanci ne zai kawo zaman lafiya mai dorewa a jihar Kaduna.
Bayan shafe shekaru masu yawa a yaki da cutar shan inna, hukumar lafiya ta duniya ta ayyana Afrika a matsayin nahiyar da ta barranta daga cutar shan inna bayan Najeriya ta samu shekaru 4 ba tare da bullar cutar ba.
Ba mamaki hankalin matasan Najeriya ya raja'a ga karanta fasahar zamani da ta hada da manhajar lataroni, ganin yadda bangaren ke ta kawo kudi a sassan duniya a yanzu.
Hukumomin gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu ba sa taimaka wa jami’o’i su rayu ta hanyar kere-kere a Najeriya, a cewar wasu kwararru.
Talakawa na shiga ragaita a birane don rashin gidaje da hakan kan sanya su zama a gidajen haya.
Zuwa karshen makon nan hedkwatar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya da ke Abuja na ci gaba da kasancewa a rufe karkashin gagarumin tsaro daga jami’an ‘yan sanda.
Domin Kari