A kusan kullum shafukan yanar gizo da jaridu, da kuma sauran kafafen labarai na nuna yadda mutane masu hazaka a Najeriya ke yin kere-keren da zasu taimaka wa kasar samun abubawan da take bukata ba tare da tafiya ketare ba.
Tun a farkon hawan gwamnatin APC a shekarar 2015, shugaba Muhammadu Buhari ya nuna takaici akan cewa hatta tsinken sakacen hakori sai an shigo da shi daga ketare.
Dakta Faruk BB Faruk, masanin siyasar tattalin arziki na jami’ar Abuja, ya ce rashin karfafawa jami’o’i gwiwa ta hanyar sayen fasaharsu na sa su kasancewa masu koyarwa akan takarda a ko da yaushe, kuma basu da hanyar samun kudin shiga sai daga gwamnati da kuma dalibai.
Dakta Faruk ya kuma ce ba girma ko yawan gine-gine ke nuna tasirin jami’a ba, amma irin binciken da ta ke gudanarwa na kere-keren fasaha.
Shi kuma masanin harkokin tattalin arziki Abubakar Ali, cewa yayi rashin samun nasara a fannin yaki da cin hanci da rashawa zai ci gaba da hana Najeriya zama cikin sahun masu arzikin masana’antu a duniya.
Bayan noma da kiwo, da kuma ma’adinan da a kan gano ta hanyar dabarun gargajiya, akasarin masana’antun Najeriya ba sa aiki yadda ya kamata, sai tarin injina masu tsatsa da ciyawa a harabar wasu kamfanonin.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum