Kwararru sun yi ittifakin cewa duk da mayar da hankali da ake ta yi kan bangaren man fetur, ba shi ne ya fi kawo kudin shiga ba. Bangaren sadarwar zamani da ake yi da fasahar lataroni da manhajojin komfuta shi ne ya fi kawo kudin shiga.
“Tazarar alkaluman raya arziki da bangaren sadarwa ke samarwa ya fi kashi 5% in an gwada ta da sashen fetur da iskar gas. Wannan na nuna ma ka wannan sashe ya na tafiya yadda ya dace.” inji ministan sadarwar Najeriya Dr.Isa Ali Pantami a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan dawowa daga taron sadarwa na duniya da a bana a ka gudanar a birnin Budapest na kasar Hungry.
Dr Pantami, wanda ya jagoranci tawagar Najeriya a taron da ya duba kalubalen sadarwa da kuma hawa kan manhajar sadarwa mafi karfi da da kuma sauri ta 5G. Ya ce yanzu zamanin samun cigaba ne na tattalin arziki ta hanyar sadarwar lataroni, wadda ake yi da fasahar manhajar komfuta da dangoginta.
Hakanan Pantami ya ce zai bi sawun matakin da ma’aikatar sa ta dauka ta hana kwarar mutane wajen shanye mu su kudin da su ka zuba a wayoyinsu ko na’urorinsu na hawa yanar gizo ta barauniyar hanya.
Shi ma shugaban hukumar bunkasa sadarwar zamani NITDA Kashifu Inuwa Abdullahi ya ba da tabbacin wanzar da abin da ya zayyana da ayyukan da su ka faro lokacin da Pantami ke babban daraktan hukumar.
Najeriya dai na da kamfanonin sadarwa da dama masu zaman kansu ciki kuwa har da MTN na Afurka ta Kudu, inda kasar ta gaza wanzar da kamfanin sadarwarta na wayar tangaraho ta girke NITEL da ta salula Mtel.
Yanzu dai abun da a ke iya gani sai dogayen karafan sadarwar kamfanin NITEL a birane da kauyuka da ma’aikatan da su ka yi ritaya da ke ba da tarihin jiya ba yau ba.
Saurari cikakken rahoton da Nasiru Adamu Elhikaya ya turo:
Facebook Forum