Majalisar koli ta addinin musulunci ta Najeriya karkashin Sultan Muhammad Sa’ad, ta ce ta na goyon bayan matakan hana yaduwar cutar Coronavisur da suka hada da kaucewa taruka masu dumbin jama’a a waje guda musamman a yankunan da ke da matukar barazanar cutar.
Bayan taron majalisar a Abuja, a zantawar da ya yi da wakilinmu Hassan Maina Kaina, mataimakin babban sakataren majalisar, Farfesa Salisu Shehu, ya ce za a gudanar da sallar juma’a a babban masallacin Abuja.
“Duk matakan da ake dauka na killace mutanen da suka kamu da kuma kare wadanda ba su kamu ba, matakai ne da addinin musulunci ya amince da su,” a cewarsa.
Ya kuma kara da cewa, “za a yi sallar juma’a, a wannnan babban masallaci na Abuja saboda haka jama’a a fita a yi sallar juma’a musamman a garuruwan da ba su da alamar bullar cutar.”
Za a jira zuwa sallar jumma’a a ga masallatan da za su gudanar da sallah da wadanda za su kauce wa hakan.
In za a tuna shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce addinin musulunci ya amince da kauce wa duk sassan da ke da barazanar wata cuta.
Gabanin wannan yanayi da rahoton samun cutar a Abuja, ita ma kungiyar Ansarul din Altijjaniyya ta dage taron maulidin Shehu Ibrahim Niass da ya kamata a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.
Zuwa yanzu dai mutum 12 ne aka gano cewa suna dauke da cutar a Najeriya.
Facebook Forum