Baya ga rashin mota ko babur, babban abinda da kan takura wa masu karamin karfi a birane musamman ma’aikata shi ne rashin muhallin kansu.
Rashin mallakar muhalli na sa masu karamin karfi tara akasarin abinda su ke samu daga aiki ko sana'o'in da suke yi su damkawa masu gidajen haya, kuma idan aka samu akasi sai ka ga an ba dan haya wa’adin tashi.
Ahmed Minista, ma’aikaci ne da ya yi zaman haya a birnin Abuja wanda a baya aka taba gurfanar da shi a gaban kotu bisa tuhumar rashin biyan haya, ya ce masu bada haya basu tausaya wa masu karamin karfi.
Bankin “Mortgage” shi ne bankin gwamnatin Najeriya da ke ba da lamuni don gina gida, mallakar gida ko gyara gidan da mutum ke ciki.
To amma ko kowanne dan Najeriya zai iya samun damar mallakar gida ta hanyar bankin?
Babban manajan bankin, Ahmed Musa Kangiwa, ya ce kowanne dan Najeriya zai iya karbar bashin gina gida, ko sayen gida, ko kuma gyaran gida in ya kai shekara goma sha takwas da haihuwa, kuma yana samun albashin da ya wuce naira dubu uku.
A birnin Abuja yanzu haka akwai manyan gidaje a unguwanni kamar Maitama da Asokoro da ba kowa a cikinsu saboda ko dai masu gidajen ba su da bukatar gidajen, ko kuma ba su da ra'ayin sanya haya.
Akwai kuma manyan gidajen da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kwace, wasu gidajen kuma ana zargin an gina su ne don boye kudin almundahana maimakon barin kudin a banki da hakan ka iya jan hankalin hukumomin kasar.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum