Monguno dai ya nuna an sauya ma sa manufar bayanan kalamun sa, ya ce "shugaban kasa ya yi iya kokari, ya ba da kudade na fitar hankali amma ba a sayo kayan ba."
Tuni dai fadar gwamnatin Najeriya ta ce sam ba wasu kudin makamai da su ka salwanta a zamanin tsoffin manyan hafsoshin na ta, wanda hakan ya saba da yanda ta zargi tsohuwar gwamnati Jonathan ta ofishin tsohon mai ba da shawara Kanar Sambo Dasuki da almubazzaranci da kudin makamai.
Karin bayani akan: Babagana Monguno, Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Amma masu sharhi sun ce suna bukatar a kaddamar da bincike kamar yanda a ka yi ga tsoffin manyan hafsoshin Jonathan irin su marigayi Alex Badeh.
A hirar shi da Muryar Amurka, Attahiru Bafarawa tsohon gwamnan Sokoto ya ce ana sa ra'ayin Allah ya yi wa shugaba Buhari gyadar dogo da irin wadannan bayanai su ka fito fili tun ya na kan kujerar mulki.
Gwamnatin Buhari dai ta zo kan mulki ne a 2015 kan alwashin yaki da cin hanci da rashawa shi yasa ake sa ran za ta fito da wannan bincike don gane mai laifi ko wanda ba shi da laifi.
Alamun gamsuwa da shugaba Muhammadu Buhari ya yi da tsoffin manyan hafsoshin, shi ne ya sa ya nada su a matsayin jakadun Najeriya a ketare mako daya bayan ya sa su ajiye aiki.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya cikin sauti: