A hirar shi da Muryar Amurka, ta wayar tarho daga daji inda ya ke tsare da daliban 17 bayan kashe 5 daga ciki, Baleri ya ce ranar talata zai dau mummunan matakin matukar ba a turo sakon ba.
Baleri wanda ke nanata cewa da gaske ya ke yi wajen barazanar, ya bayyana cewa yanzu haka akwai mata 15 da maza biyu a hannun su da su ka hada da jikan marigayi sarkin Zazzau Shehu Idris mai suna Hamza.
Yayin da Baleri ke cewa iyayen yaran sun turo mu su diyyar da ta kai naira miliyan 45, ya ce sun sassauto daga wajen Naira miliyan 600 da su ka nema tun farko, yanzu su na bukatar miliyan 100 kuma sun yi amfani da kudin da a ka fara turowa wajen sayawa yaran garin kwaki.
Karin bayani akan: sarkin Zazzau Shehu Idris, Muryar Amurka, Jami'ar Greenfield, Kaduna, Naira, Baleri, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
Madugun barayi Baleri ya ce wannan shi ne wa'adi na karshe da zai bayar na yau litinin din nan.
Har yanzu akwai daliban kolejin kimiyyar gandun daji da ke hannun wasu gungun barayin da hakan ya maida jihar Kaduna mafi fama da kalubalen barayin mutane.
Gwamnatin Kaduna na nanata ba goyon bayan biyan kudin fansa.
Saurari cikakken rahaton a sauti: