A Najeriya jama'a na ci gaba da fuskantar matsanancin yanayin zafi, musamman a arewacin kasar wanda ke sa wasu Musulmi dake azumi shiga cikin damuwa.
A Najeriya bisa ga yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar jama'a kuma kusan ta gagari magani, ‘yan kasar na shawartar mahukunta da su waiwayi shawarwarin da aka bayar a baya a gwada amfani da su ko da za ta samu saukin matsalolin.
A Najeriya matsalolin rashin tsaro na ci gaba da tayar da hankulan jama'a domin a nasu ganin kamar lamarin ya gagari mahukumta, amma dai suna kara kiraye kirayen samun dauki.
A Najeriya yadda ake sako-sako da daukar matakan hukunta masu aikata laifukka na ci gaba da ingiza jama'a wajen aikata wadannan laifuka duk da hadarin da ke tattare da aikata su.
Wani abu da ya fara jan hankalin jama'a shine ganin ‘ya'yan wadanda suka saba rike madafun iko a can baya da suke son suma su shugabanci jama'a.
A daidai lokacin da yakin da ake yi tsakanin Kasashen Rasha da Ukraine ke ci gaba da zama sanadin salwantar rayukan jama'a, tuni wasu miliyoyin mutane suka kubuta ta hanyar ficewa daga kasar.
A Najeriya jama'ar kasar na ci gaba da fuskantar wasu matsaloli da ke sanadin salwantar rayukan jama'a ta fuskoki daban daban, kamar yadda wata gobara da ta kama wani kamfanin siminti ta yi sanadin salwantar rayuka a Sakkwato dake arewa maso yammacin kasar.
Matsalolin rashin tsaro a Najeriya na ci gaba da mamaye sassan kasar, suna ta illata yankunan arewa da jama'ar yankin.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan sanda suka yi musayar wuta da 'yan bindigar yayin da suke kokarin kubutar da wasu 'yan kasar waje a kamfanin sarrafa tumatir da ke garin Ngaski.
A Najeriya matsalolin rashin tsaro na ci gaba da tayar da hankulan jama'a inda har su ka fara yanke kauna ko za su fita daga yanayin.
A Najeriya iyalan jami'an tsaron da aka kashe a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin kasar, sun gudanar da zanga zanga.
A Najeriya kididdiga ta nuna adadin masu kwankwadar miyagun kwayoyi ya haura mutum miliyan goma sha biyar abinda ya sa kasar ke sahun gaba ga yawan masu amfani da miyagun kwayoyi.
A Najeriya bisa ga yadda matsalolin rashin tsaro ke ci gaba da wanzuwa kuma duk da kokarin da ake yi ya kasa shawo kan matsalar, ya sa ake ci gaba da lalubo hanyoyi daban-daban ko da za'a samu dacewa.
Hukumar hana fasa kwabri ta damke wasu mutane biyu a jihar Kebbi da suke tuhuma da yanka Jakuna kimanin dubu daya da aka kiyasta kudin su fiye da naira miliyan 42 suka yi safarar naman su.
A Najeriya har yanzu ana ci gaba da samun asarar rayuka masu tarin yawa sanadiyar ayukan ‘yan bindiga.
A Najeriya rikice-rikicen siyasa na ci gaba da daukar hankalin ‘yan kasar daidai lokacin da ake kara matsawa ga shekarar da za'a gudanar da zabubukan shekara 2023.
A Najeriya wasu jama'a na ganin cewa lokaci ya yi da ya kamata jama'a su bullo da hanyoyin da za su ceto kasar da rayukan ‘yan kasa daga matsalolin da suke neman wargaza kasar tunda gwamnatoci sun kasa saukar da nauyin da ke kansu na aza ta bisa turbar cigaba.
A daidai lokacin da ake sa ran fara dauko dalibai ‘yan Najeriya da yaki ya rutsa da su a Ukraine, wasu iyayen yaran na fatar ganin yaran sun iso lafiya.
Har yanzu dai ‘yan Najeriya musamman na arewacin kasar sun kasa samun mafita daga matsalolin rashin tsaro dake hana su yin bacci da ido biyu a rufe.
A Najeriya Mahukuntan kasar sun ce suna da amannar cewa habaka harkokin wasanni zai taimaka wajen kara samar da hadin kan kasa da wanzar da zaman lafiya da aka jima ana lalaben hanyoyin samun wanzuwarsa.
Domin Kari