Jihar Sokoto, na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalolin rashin tsaro baya ga Kaduna, Katsina, Zamfara da Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
A Najeriya duk da alkawullan da shugaban kasar Muhammad Buhari ya sha nanatawa na hannunta kasa mai cikakken tsaro ga gwamnatin da zata gade shi, har yanzu jama'a na ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci a yankuna daban daban.
A Najeriya, irin wadannan kungiyoyi su ne suka yi ta fafatuka har suka nemowa kasar ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Tarihi ya nuna cewa a arewacin Najeriya tun kafin zuwan turawan mulkin mallaka, akwai zaunannen tsarin shugabanci wanda daular Usmaniya ta assasa.
Dangin Magajin garin Sokoto Hassan Ahmad Danbaba sun tabbatar da rasuwar sa ranar Asabar bayan gajeruwar rashin lafiya.
A Najeriya al'ummomin da suka fuskanci matsalolin rashin tsaro a baya sun fara kokawa domin matsalar ta soma waiwayowa a 'yan kwanakin nan.
A Najeriya batun cunkoso a gidajen gyara hali ya jima yana daukar hankalin jama'a kuma duk da kokarin da mahukunta ke yi don magance matsalar har yanzu ana samun cinkoso.
Rikice rikicen siyasa na ci gaba da daukar hankalin jama'ar Najeriya daidai lokacin da lokutan gudanar da zabubuka ke kara matsowa.
Wani abu da ke jan hankalin ‘yan Najeriya bai wuce batun shugabancin kasar ba, inda wasu ke ganin ya kamata a yi karba-karba tsakanin yankin kudu da arewa, wasu kuma na ganin akasin hakan.
A Najeriya al'ummomin kasar na cigaba da fuskantar hare-haren ta'addanci daga ‘yan bindiga abinda har sun wasu daga cikinsu sun fara yanke kauna ga kawo karshen matsalolin, kawai suna jiran yadda Allah zai yi dasu.
Matsalolin cin zarafin bil'adama na ci gaba da wanzuwa a sassan Najeriya, ciki har da safara da kuma satar kananan yara. Jami'an tsaron DSS a Najeriya sun ceto wasu yara hudu da aka sace daga arewacin kasar aka sayar da su a yankin kudu.
Da yawan jama'a na dora alhakin koma-bayan kasar ga dalilai mabambanta, da kuma hanyoyin da suke ganin za'a iya samun mafita.
Haren-haren ta'addanci na ci gaba da zama sanadiyar rashin rayuka da dukiyoyin jama'a a Najeriya musamman a arewacin kasar.
"Yanzu har shigar burtu suke yi, su yi shigar mata su saka hijabi, su shiga gari su labe. Kullum abin da ke faruwa kenan." In ji Isa Ambarura.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da kungiyoyin fafatuka ke ta faman fadakar da jama'a akan illolin shaye-shayen kayan da ke sa maye.
A Najeriya rikice na kara fadada a cikin jam'iyyar APC mai mulkin kasar duk da yake lokaci sai kara matsawa yake yi ga shirye-shiryen zabukan shekara ta 2023.
Ranar Asabar wani rukuni na daliban da aka sace a makarantar Sakandaren birnin Yauri ta jihar Kebbi ya iso a fadar gwamnatin jihar.
A Najeriya sarakunan gargajiya sun jima suna korafi akan ba su da wani tanadi na aikin da kundin tsarin mulkin kasar ya ba su wanda za su bayar da gudunmowa ga ci gaban al'umar kasa.
A Najeriya, alamu na nuna cewa akwai yiwuwar a samu saukin matsalolin rashin tsaro a wasu yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga saboda a baya bayan nan ana jimawa ba tare da an kai hari ba a wasu wuraren, sai dai kuma ana fuskantar kananan hare-hare a wasu wurare dabam.
A Najeriya daidai lokacin da shekara ta 2022 ke dab da shigowa wadda ita ce jajibirin shekarar zabubuka a kasar, alamu na nuna wankin hula na neman kai dare ga jam'iyar APC mai mulkin kasar domin ta kasa sasanta rikice-rikice da ke ci gaba da tarwatsa ta.
Domin Kari