Hakan na zuwa ne lokacin da ‘yan bindiga ke ta cin karensu babu babbaka a wasu yankunan arewacin kasar.
Jama'ar arewacin Najeriya na ci gaba da kokawa akan matsalolin rashin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa ganin a yankunan kullum sai tabka hasarori ake yi sanadiyyar ayyukan 'yan bindiga.
A jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin kasar wasu mahara sun tare hanyar garin Goronyo da ke gabashin jihar jiya Lahadi, ranar da kasuwar garin ke ci, abin da ya kara daga hankalin jama'a, musamman duba da wani hari da suka saba kaiwa a kasuwar wanda yayi sanadin salwantar rayuka da dama.
Wannan lamarin ya faru ne kasa da mako daya da gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal ya katse wata ziyara da ya kai a Abuja ya dawo Sakkwato saboda wasu bayanan da ya ce ya samu dangane da abin da ke faruwa a wani kauye da ke yankin Wurno har ma ya ja kunnen jama'ar garin da su kansu ‘yan ta'addar.
Sai dai wannan bai hana barayin aika aikar su ba a gabashin jihar domin a Illela domin bayanai sun nuna har yanzu jama'a na zaman dar dar kamar yadda wani dan yankin ya shaida wa Muryar Amurka.
Wannan yanayin ya sa jama'ar ke ta kiraye kiraye ga mahukunta akan a kawo musu dauki.
Duk kokarin jin ta bakin jami'an tsaro ya ci tura.
Irin wannan yanayin na ci gaba da wanzuwa a wurare da yawa a arewacin Najeriya abin da ke dada jefa rayukan jama'a cikin kaka-ni-kayi.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: