Wannan na zuwa ne lokacin da ‘yan ta'adda ke ci gaba da yin barazana ga rayukan jama'ar kasar musamman jihohin arewa.
Matsalar rashin tsaro dai yanzu a iya cewa ta zamo abokiyar zama ga ‘yan Najeriya musamman a yankin arewa domin kusan kullum sai an samu rahoton wata aika-aika da ‘yan bindiga suka tafka.
Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin kasar ma duk maganar daya ce, domin jama'a na ta fuskantar matsalolin har a cikin wannan wata na Ramadana.
Yankin Rabah, Mahaifar firimiyan arewacin Najeriya Sir Ahmadu Bello Sardauna yana jima yana fama da wannan matsalar, inda jama'a ke ta kokawa.
Dokta Abdullahi Alhaji Zakari, wakilin jama'ar Rabah a majalisar dokoki ta jihar Sokoto, ya ce cikin wannan satin ma, an kai masu hari, inda cikin mutanen da ake kashewa, mafi aksari 'yan banga ne.
Wani abin tashin hankali a cewar dan majalisar shi ne yadda ake kashe jami'an tsaro na banga wadanda suka sadaukar da rayukansu duk da karancin taimako da suke samu.
A watannin baya gwamnatin jihar ta sha alwashin baiwa jami'an na banga alawus na wata wata don kara karfafa musu gwiwa.
Muryar Amurka ta zanta da Sakataren kungiyar ta banga a jiha, inda ya ce a gaskiya ana kashe masu mutane sosai, kuma har yanzu ba a fara ba su ba ko da shike, satin da ya gabata, an kira su an ce za a fara ba su.
Kwamishinan lamurran tsaro a jihar ta Sokoto, Kanal Garba Moyi mai ritaya ya tabbatar da ana samun kai hare-hare a wasu yankuna tare da satar mutane.
Masu lura da lamurran yau da kullum da ma su kansu mahukunta, na karfafa gwiwar Musulmi akan su dage da addu'o'in samun saukin matsalolin musamman a wannan wata mai alfarma.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: