Wannan karon jami'o'i ne ke ganin akwai gudunmuwar da za su bayar, kamar jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto wadda yanzu haka ke shirin hada kan al'ummomin Fulani na nahiyar Afrika da manufar samo bakin zaren warware matsaloli.
Tun lokacin da matsalolin rashin tsaro suka soma gagarar mahukunta a Najeriya al'ummomi da kungiyoyi dama wasu hukumomi ke ta fadi-tashi wajen marawa gwamnati ko da za'a samu bakin zaren warware matsalolin da ke mayar da hannun agogo baya ga ci gaba kasar da jama'arta.
Bayan bayar da ilimi da tarbiya da suke yi ga jama'a, jami'o'i suna wasu ayukka na taimakon al'umma a wasu fannonin rayuwa.
Hakan ne ma ya sa jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sokoto ta shirya taron manazarta wakoki cikin harshen Hausa don su shirya kasidu na ilmantar da jama'a akan sha'anin tsaro wanda ya gudana a bara.
Bisa ga gamsuwa da kuma duba da yadda ake nuna yatsa kan Fulani akan hannu ga matsalar ta rashin tsaro ya sa jami'ar ta soma shirin fadada shirin hada kan Fulani na nahiyar Afirka domin a tattauna a fahimci juna tsakanin su da sauran al'ummomi a kuma ilmantar da duk mai jin fulatanci akan yadda za'a samu zaman lumana.
Farfesa Aliyu Muhammad Bunza ya maganta a madadin jami'ar akan wannan shirin. Ya ce a tunkari abun kai-tsaye don ba abun da ya fi bala'i kamar kashe mutum.
Ya ce a da, da ake samun tashe-tashen hankula lokacin Usman Dan Fodio, Fulani ne ke kawo kwanciyar hankali, don haka a nemi haddin kansu.
Jigo a cikin kabilar Fulani a Najeriya kuma tsohon shugaban kungiyar Miyetti Allah ta Birnin tarayyar Najeriya Abuja, Muhammadu Dodo Oroji tuni ya yi na'am da wannan shirin.
Detective Auwal Bala Durumin Iya shugaban sashen nazarin lamurran laifuka da tsaro a jami'ar Yusuf Maitama Sule dake Kano, na ganin cewa wannan shirin zai yi tasiri sosai musamman don za'a gudanar a yaren da suke ji.
Duba da yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da addabar jama'ar Najeriya da ma wasu kasashe a duniya duk wani yunkuri da kan iya tasiri ga samun mafita kan iya kasancewa abin maraba ga kowa.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: