Matasan Arewa da wata kungiyar kare 'yancin fararen hula da dimokradiya CISLAC, sun nuna cewa dakatar da Sanata Abdul Ningi a Majalisar Dattawa, dakile 'yancin fadin albarkacin baki ne.
Sanata Abdul Ningi dai dan Jam'iyyar PDP ne kuma shi ne Shugaban Kwamitin kula da Yawan Jama'a wato National Population Committee sannan kuma Shugaban Kungiyar Sanatocin Arewa a Majalisar Dattawan.
Majalisar dattawa ta koka kan tabarbarewar harkar tsaro da ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya, ta kuma bayyana cewa, za ta kakkabe rahottani da ta yi tun shekara 2015 domin ta kai wa shugaban kasa saboda a dauki mataki na gaggawa.
Kungiyar GTA a majalisar wkilai su 60 ta fara wannan yunkurin ne tare da neman a koma tsarin Majalisa da aka yi amfani da a jamhuriya ta farko a Najeriya, saidai wani kwararre da ma wata fitacciyar ‘yar siyasa a Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan wanna yunkurin.
Majalisar Wakilan kasar ta bawa jama'a hakuri kan matsalar tsananin rayuwa da sha'anin tattalin arziki ya sa ake fama da ita, inda ta sha alwashin magance lamarin cikin gaggawa.
An kama Badejo ne bayan ya kafa wata kungiyar 'yan sa-kai ta Fulani zalla, domin taimakawa wajen inganta tsaron mambobinta a jihar Nasarawa da ma wasu wurare da ake fama da matsalar tsaro.
Majalisar Dattawa ta sake gayyatar daukacin jami'an tsaron kasar a mako mai zuwa domin tattaunawa tare da samar da mafita kan matsalar rashin tsaro da ta addabi kasar.
Najeriya ta yi Allah Wadai da ficewar Jumhuriyar Nijar, Mali da Burkina Faso daga Kungiyar ECOWAS ko CEDEAO duk da cewa ya zuwa yau Kungiyar ta ce ba ta samu wata sanarwar ficewar kasashen ba.
Kungiyoyin dai sun yi kira da a hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin domin ya zama izina ga wasu.
Majalisar Dokokin Najeriya ta sake amincewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ciwo wasu bashi da ya kai Dalar Amurka Biliyan 8.2, kwatankwacin Naira triliyan 7.5 domin lamuni na dogon zango.
Mataimakin shugaban Kwamitin Kasafi na Majalisar Dattawa, Sanata Mohammed Ali Ndume, ya ce sun yi aiki tukuru, ba dare ba rana domin sun gano wurin da aka yi ta jita-jita cewa, an fifita yankin kudu kan yankin arewa a kasafin kudin 2024.
Domin Kari