Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bada 'yanci game da bayyana ra'ayi amma kuma akwai iyakoki.
Al'ummar yankin Mubi da aka kwati daga hannun 'yan Boko haram na fuskantar karancin jami'an kiwon lafiya.
Ma'aikatan shari'a a jihar Kano sun ce ba zasu koma bakin aiki ba har sai gwamnatin tarayya ta saurare su ta kuma cimma burinsu.
Bata gari ne suka haddasa rikicin da ya faru a karamar hukumar Mangu.
Jam'iyyun hamayya da sauran jama’a na da damar kai korafin su kotu duk lokacin da aka karya wata doka.
Ana dab da shiga shekarar 2015, wasu na bayyana tsammanin su akan shekarar yayinda ake ta bankwana da shekarar 2014.
Wasu na murnar haihuwa wasu kuma ba sa so. labarin wani mutum ke nan da matarsa
Hukumar bada agaji da gwamnatin tarayya sun fito da wani shiri na bude makarantu a sansanonin 'yan gudun hijira, don kada a bar yaran da rikicin 'yan boko haram ya shafa a baya.
A tabbatar da cewa jami’an da za sa ido wajen zabe na jam’iyyun adawa da mai mulki ba wadanda zasu haddasa fitina ba ne, ko suyi burus da ka’idodin zabe da hukumar zabe ta shimfida- innji Dr. Abbati
Yanzu haka wata sabuwa ta sake kunno kai a jihar Taraba dake Najeriya game da zargin da akewa mukaddashin gwamnan jihar cewa akwai wata kullaliya a tsakaninsa da yar takarar gwamna ta jam’iyyar adawa ta APC
Batun ba kananan hukumomi cin gashin kansu ya haifar da cece-ku-ce, Yayinda majalisun dokoki suka kammala aikinsu
Hanyoyin da za a iya magance matsalolin Najeriya shine kawas da kabilanci, bam-bancin addini, da sauransu musamman yanzu da ake shirin yin zaben shekarar dubu biyu da goma sha biyar.
Da dumi duminta, wani bom ya tashi a wata kasuwa a jihar Bauchi amma ba a san adadin wadanda suka mutu ko jikkata ba.
Ana shirin karin kudin haraji akan kayayyakin saye da sayarwa har kashi goma daga kashi biyar, da kuma tsaurara mayakan canjin kudade musamman dala.
Rikicin jihar Nasarawa tsakani kabilu, yayi sanadiyar daidata al'ummar wasu garuruwan, wanda ke gudun hijira yanzu haka. abinda wasu ke gani hakan zai iya shafar zabe mai zuwa a jihar.
Karo na biyu ke nan ana tada Bom a tashar mota a jihar Gombe wanda ya janyo hasarar rayuka da raunata mutane da dama.
A fannonin al'umma daban da ban, mata suma suna taka muhimmiyar rawa kamar siyasa, ilimi da kasuwanci. Wata mace mai kamar maza na bada shawarwari ga matasa akan irin sana'o'in da suke sha'awa.
Unguwar zoma yau ta dan sha banban da ta da, inji wata mata da ke sana’ar a jihar Kano.
'Yan gudun hijir da dama da rikicin arewa maso gabashin Najeriya ya dai-daita na kira da a kwato masu garuruwansu kafin zabe mai zuwa don su samu su yi zabe.
kungiyoyin mata sun tashi haikan wajen wayar ma 'yan uwansu mata kai akan zabe.
Domin Kari