Fiye da makonni shidda da kwato yankin Mubi dake jihar Adamawa daga hannun mayakan kungiyar Boko haram, ya zuwa yanzu dai yankin na fuskantar karanchin malaman kiwon lafiya da kuma wasu hukumomin gwamnati.
Wasu daga cikin wadanda suka koma yankin kuma na fuskantar matsalolin kiwon lafiya. Har ma al’ummomin yanki na kira ga gwamnati da ta taimaka ta dawo da ma’aikatan bakin aikinsu.
Ganin halin da jama’ar ke ciki ya sa kungiyar bada agaji ta Red Cross tura jami’anta domin taimaka ma al’umomin da suka koma.
Wasu shugabannan yankin suma suna haramar kai tallfin kayayyakin jinya, a yankin. Dan siyasa Alhaji Abdulraham Gwajam, ya yi kira ga gwamnatin jihar Adamawa da taimka ta sa shugabannan kananan hukomi da sauran kusoshin yankin komawa su zauna da ‘yan garin.
Ya zuwa yanzu dai akwai sauran yankunan da ke hannun ‘yan boko haram, wato garuruwan Michika da Madagali kuma dubban ‘yan gudun hijirar da suka fito daga yankin na cikin mawuyacin hali.
Mai shari’a Ahmad Ali Gulam, tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkokin siyasa yace kashi saba’in cikin dari din yan yankin na gudun hijira yanzu haka. Kuma ya kara da yin kira ga gwamnati da ta taimaka ta dawo da 'yan yankin a kuma tamaka masu da abinci.