Da yake jawabi a taron gangamin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a birnin Sokoto, gwamna Aliyu Magatakarda Wamako yayi kakkausar suka akan kalaman da mai ba shugaban kasa shawara akan sha’anin tsaro yayi, na bukatar dage gudanar da babban zaben watan gobe. Abinda gwamnan ya bayyana a zaman wani yinkuri na kawo cikas a tsarin zaben.
Dalilin wannan kiran da mai ba shugaba shawara yiyi shine ganin cewa har yanzu ba a gama rarraba katun did-din-din na zabe ba kuma zaben na karatowa.
Haka shi ma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC Janar Mohammadu Buhari mai ritaya, ya fadi cewa wannan hurumin hukumar zabe ne ta dage zaben in da bukatar yin haka ba ra'ayin wani ba.
Da alama dai cincirundon taron jama’a a gangamin yakin neman zabe a jihohiin sokoto, Kebbi da Zamfra da aka yi ya gamsar da Janar Buhari, wanda ya bayyana cewa da alamun nasara amma yana ganin akwai sauran aiki a gaba.
Shi ma shugaban jam’iyyar APC ta kasa chief John Oyegun, ya nuna mamakinsa ganin yadda ya ga taron jama’ar na neman canji a kasar.