A jiya ne kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya ta umurci ‘yayanta a kasa baki daya da su tsunduma cikin yajin aiki. Biyo bayan abinda ta kira rashin mutunta umurnin kotu da gwamnatin tarayya tayi game da batun hakkokin ‘yan kasar.
A yanzu haka dai kotuna na rufe a duk fadin birnin Kano biyo bayan wannan umurnin.
Malam Mukhtar Rabi’u Lawan, shugaban kungiyar ma’aikatan sharia na reshen jihar Kano, ya tabbatar ma wakilin muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari cewa ba za su koma bakin aiki ba har sai gwamnatin tarayya ta biya masu bukatunsu.
A jihar Ogun kuma, reshen Kungiyoyin ma’aikatan shari’ar na ganin cewa yajin aiki ba shine abin da ya dace ba, maimakon haka kamata yayi su koma kotu domin tilasta ma gwamnati aiwatar da kudirin da ta dauka na kotu.
Sai dai kuma wannan ra’ayin ya saba ma kungiyar lauyoyi ta reshen jihar Kano. Dr. Mamman Lawan Yusufari, shugaban kungiyar lauyoyin jihar Kano, ya fadi cewa ma’aikatan na da damar yin yajin aiki don a bi masu hakkin su.