A watan Yunin shekarar da ta gabata ne ‘yan kungiyar Boko haram suka sace wani dan kasar Jamus Mr. Robert Nitsch Eberhard kusa da masaukinsa da ke cikin garin Gombi a arewacin jihar Adamawa, daga bisani kuma kungiyar ta fidda sanarwar cewa ita ta sace shi.
Yanzu haka dai al’ummar garin Gombi na cike da farin ciki game da kubutar da mutumin da aka yi ranar Talatar da ta wuce. Jama'a da yawa sun shaida cewa garin na cike da farin ciki saboda irin kyawawan halayar Mr. Robert.
Al’ummomin yankin Gombi da sauran wuraren da aka kwato daga hannun ‘yan boko haram a arewacin jihar Adamawa na cigaba da maida murtani game da kiran da gwamnan jihar Mr. Bala John Ngilari yayi na cewa ya kamata a dage batun zaben watan gobe har zuwa watan Afirilu.
Ga dukan alamu dai bana za a sami sauyi a jihohin Adamawa da Taraba ganin yadda jama’a suka zaku da kuma shirya wa zaben.