Shugaban Amurka Donald Trump ya sake hurawa ‘yan majalisar dokokin kasar wuta akan su amince da batun gina ganuwa akan iyakar Amurka da Mexico, don magance shigowar bakin haure, batu mai cike da takaddama a kasar.
“Tsaron iyaka tsaron kasa ne,” a cewar Trump a lokacin da ya ke jawabi a wani taron manema labarai da aka yi a fadar White House bayan ganawar sa da firayin ministan Italiya Giuseppe Conte, shi ma wani shugaban da ya ke daukar tsauraran matakai akan shige da fice a kasar sa. Trump ya kuma ce, “dole ne kasashe masu karfi su kasance da iyakoki masu karfi.”
Da yake karin bayani akan kalaman da yayi geme da shige da fice a shafin sa na twitter jiya, Trump ya ce ba ya da matsalar dakatar da ayyukan gwamnati a karshen watan Satunba a lokacin da wa’adin kashe-kashen kudade na shekara ke karewa, idan har bai sami amincewar gina ganawar ba, daya daga cikin muhimman alkawulan da yayi a lokacin yakin neman zabensa a shekarar 2016.
Facebook Forum