Wani rahoto daga wata jaridar Amurka da ta yi suna ya ce, shugaba Donald Trump ya umurci manyan jami’an diplomasiyyarsa akan su duba hanyar yin tattaunawar kai tsaye da ‘yan Taliban, a kokarin da ake yi na fara zaman shawarwari da kungiyar mayakan da zummar kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 17 ana yi a Afghanistan.
Jaridar New York Times ta fada jiya Lahadi cewa wannan matakin na zaman wani gagarumin canji a manufofin Amurka a Afghanistan.
Jaridar ta kuma ce, manyan jami’an Amurka sun je Afghanistan da Pakistan kwanan nan, inda suka tattauna da wasu wakilai na kasashen biyu don shirin yin ganawar kai tsaye da ‘yan Taliban din.
Rahoton ya kuma ce ana cigaba da samun amincewa tsakanin jami’an Amurka da na Afghanistan akan cewa, hanya daya za a fara shirin samar da zaman lafiya da kuma cimma yarjejeniyar karo karshen yakin, ita ce Amurka ta jagoranci zaman shawarwarin kai tsaye.
Facebook Forum