Rayuka da dama sun salwanta a shekarun baya sakamakon bullar cutar Ebola, amma maganin rikafin cutar da aka samo yanzu zai taimaka matuka wajen dakile cutar.
Wani jami'in lardin Ghazni ya fada yau Talata cewa, 'yan kungiyar Taliban sun iya kwace gundumomi biyu, Jaghatu da Dehak, bayan wani mummunan fada a daren jiya.
Amurka ga gargadi Iran ta sauya dabi'unta idan ba haka ba zata dauki matakan matsin lamba kan kasar. Sai dai ba a fayyace iya matsin lambar da Amurka zata iya yi, ba tare da kasashen Turai ba, dake aiki da Iran don ceto yarjejeniyar Nukiliyar.
Jami’an koriya ta kudu sun fada ranar Lahadi cewa Kim ya shirya zai gayyaci kwararru, da ‘yan jarida daga koriya ta kudu da Amurka don su kasance wurin a lokacin da za a rufe cibiyar.
Amma fadar shugaban Amurka ta ce ta ba mashawartan kasar karin kwanaki 30 su nemi yarjejeniyar da za a iya cimmawa.
Babu wasu hujjoji da ke nuna cewa Iran ta cigaba da yinkurin kera makaman nukiliya bayan shekarar 2009.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban Amurka Donald Trump yau Litinin a birnin Washington DC, wannan ne karon farko da wani shugaba daga nahiyar Afrika ya kai ziyara fadar White House a wannan shekarar ta 2018.
A Janhuriyar Nijar kungiyar makiyayan arewacin yankin Tilabery ta koka akan mawuyacin halin da suka shiga sakamakon tabarbarewar al’amuran tsaro inda fadan kabilanci ke haddasa asarar dimbin rayukan jama’a.
A yau ne shugaba Muhammadu Buhari zai gana da shugaba Donald Trump a fadar gwamnatin Amurka dake birnin Washington, amma 'yan jam'iyyar adawa na gani babu abin kirkin da za a kulla a ziyarar.
Yanzu haka ana binciken wani jami'in diflomasiyyar Amurka akan wani hadarin mota da ya faru a Pakistan.
Biyo bayan kuri'ar goyon bayan da Pompeo ya samu, ana kyautata zaton zai sami amincewar duk 'yan majalisar dattawan Amurka.
Batutuwan Siriya da cinikayya na cikin abubuwan da ake sa ran shugabannin biyu zasu tattauna a ganawar da za su yi.
Kafin a kwantar da shi asibiti, Bush ya halarci jana’izar matarsa Barbara, wadda ta rasu cikin makon da ya gabata tana da shekaru 92 da haihuwa. Bush da matarsa sunyi shekaru 73 da yin aure.
‘Yan sandan kasar Canada na kokarin gano musabbabin wannan harin na jiya Litinin wanda ya kuma raunana mutane 15.
A shekara ta 2015 aka fara samun bazuwar kutsen a fadin duniya a cewar Amurka da Burtaniya kuma ta yiwu a cigaba da fadada shi don kaddamar da munanan kutse.
Trump da Abe ba bakin juna bane. Firayin ministan Japan shi ne shugaban wata kasa da shugaban Amurka ya taba ganawa da shi ido-da-ido ya kuma yi magana da shi a lokuta da dama.
Domin Kari