Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Bude Ofishin Jakadancin Eritrea a Habasha


Bude ofishin jakadancin shine ya kawo karshen ziyarar kwanaki uku da Isaias Afwerki, shugaban Eritrea ya kai Habasha.

Kasar Eretria ta sake bude ofishin jakadancin ta a Habasha. Bude ofishin da aka yi yau litinin na zuwa ne mako guda bayan da kasashen biyu suka ayyana kawo karshen yaki na kan iyaka da aka kwashe shekaru 20 ana yi, abinda yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

Firayin ministan kasar Habasha Abiy Ahmed ya mikawa shugaban kasar Eretria, Isaias Afwerki makullan ofishin jakadancin dake Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Dubban mutane sun nuna farin cikin su jiya Lahadi a Addis Ababa a yayinda Abiy ya rungume Isaias a wajen wani bikin raye-raye da kade-kaden murnar yarjejeniyar da kasashen biyu, dake yaki a baya suka rattabawa hannun.

“Kiyayya, da wariya, da kuma zagon kasa sun kare yanzu, “abinda Isaias ya fadawa yan Habasha kenan idanuwan shi cike da hawaye. Ya kuma ce, a shirye muke mu yi aiki tare da “ku” don samun cigaba. Babu wanda zai lalata kaunar da muka farfado da ita yanzu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG