Kazalika gwamnonin sun kara jaddada matsayarsu ta cewa Najeriya ta ci gaba da zama a matsayin kasa dunkulalliya bisa tsari na adalci.
“A irin duniyar da nake rayuwa, idan ka ce sai da safe, ba ka sake komawa ka ce ina wuni." In ji Obasanjo.
Yankin garin Zaria a ‘yan kwanakin nan yana yawan fadawa tarkon ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa.
Dubban mutane ne ke zaune a sansanin ‘yan gudun hijira da ke kananan hukumomin Kukawa, Marte, Bama, Gwoza da Ngala.
Shugaban Najeriya ya yi kira ga daukacin ‘yan kasar da sauran al’umar duniya da su taya Paparoma da addu’a.
A ‘yan kwanakin nan an yi ta tafka muharawa a Najeriya musamman daga bangaren ‘yan adawa kan cewa gwamnatin Buhari tana cin bashin da ya wuce kima.
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas da ke Kudu maso yammacin Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa wata matashiya ta mutu sanadiyyar harbin da suka yi don tarwatsa masu zanga-zangar kafa kasar Yarbawa.
Rahotanni sun ce Sunday Igboho da jami'an tsaro ke nema ruwa a jallo, bai halarci gangamin ba.
Kwantiragin Lionel Messi a Barcelona ya kare a ranar 30 ga watan Yuni, abin da ke nufin dan wasan wanda dan asalin kasar Argentina ne na zaman kansa kenan.
“Muna kira ga Adeyemi/ Igboho da ya mika kansa ga ofishin jami’an tsaro mafi kusa. Sannan masu yabon sa, su ba shi shawara da ya yi abin da ya kamata. Ya mika kansa ga hukumomi.”
A ‘yan watannin baya, Maryam Booth ta wallafa a shafinta na Instagram cewa a taya mahafiyarta da addu’a saboda za a yi mata aiki.
Kazalika sanarwar ta yi kira ga gwamnatin Birtaniya, da ta tashi tsaye ta kare Nnamdi kanu wanda dan kasarta ne.
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP wacce Matawalle ya hau mulki karkashinta, ta yi barazanar kalubalantar gwamnan a kotu.
Yanzu Ingila za ta hadu da Sweden ko Ukraine, wadanda za su kara nan ba da jimawa ba a birnin Glasgow.
Kanu zai sake bayyana a gaban kotun a ranar 26 ga watan Yuli don ci a gaba da sauraren shari'ar.
A cewar Malami, an yi nasarar cafke shi ne tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol.
Yanzu Switzerland za ta hadu da Spain wacce ta lallasa Croatia ita ma da ci 5-3.
Afirka ta Kudu ita ce kasar da ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar ta COVID-19 a nahiyar Afirka.
Domin Kari