Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El Rufai Ya Kafa Kwamitin Binciken Ayuba Wabba, NLC Kan Yajin Aikin Watan Mayu


Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai)
Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El Rufai (Facebook/El Rufai)

An ba kwamitin kwana 60 ya kammala aikinsa daga ranar da ya fara zaman farko inda zai mika rahoto da shawarwari kan matakin da ya gwamnati ta dauka.

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufai ya kafa kwamitin bincike wanda zai duba al’amuran da suka faru a lokacin yajin aikin gargadi da kungiyar kwadago ta NLC ta jagoranta a watan Mayu.

Jihar Kaduna ta fuskanci yajin aiki na gama gari a tsakanin ranakun 16 zuwa 19 ga watan Mayun 2021, lamarin da ya kai ga dakatar da harkokin yau da kullum na tsawon kana hudu.

“Kwamitin binciken mai mambobi bakwai zai samu jagorancin tsohon mai Shari’a justice Ishaq Bello, wanda zai mayar da hankali kan duba halarcin yajin aikin da ko an take dokokin da suka shafi cinikayya da sauran ayyuka.” Wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin El Rufai, Muyiwa Adeyeke ta ce.

Ga mambobin kwamitin:

1- Hon. Mr. Justice Ishaq Bello – Shugaban Kwamiti

2- AVM Rabiu Dabo - Kwamishina

3- Mr. Eyo O. Ekpo - Kwamishina

4- Mrs. Joan Jatau-Kadiya - Kwamishina

5- Mr. Chom Bagu - Kwamishina

6- Dr. Nasirudeen Usman - Kwamishina

7- Malam Mohammed Isah Aliyu - Kwamishina

Binciken kwamitin har ila yau zai hada da duba rawar da wasu masu ruwa da tsaki suka taka gabani, a lokacin da kuma bayan yajin aikin.

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a wajen zanga-zangar (Twitter/NLC)

Sanarwar ta lissafo a matsayin masu ruwa da tsaki kamar “kungiyar kwadago da mukarrabanta, Kamfanonin wutar lantarki ta TCN, da KAEDECO, Hukumar jirgin kasa ta NRC, hukumar kula da filin tashin jirage ta FAAN, ma’aikatar sufuri ta tarayya, Mr. Ayuba Wabba, jami’an ‘yan sanda da ma’aikatar sufurin jirage ta tarayya.”

An ba kwamitin kwana 60 ya kammala aikinsa daga ranar da ya fara zaman farko inda zai mika rahoto da shawarwari kan matakin da ya gwamnati ta dauka.

An kai ruwa tsakanin kungiyar kwadago ta NLC da gwamnatin jihar Kaduna kan sallamar wasu ma’aikatan jihar daga aiki, lamarin da ya kai ga wani yajin aikin gargadi da kungiyar ta NLC ta kira, wanda ya kassara harkokin yau da kullum a jihar ta Kaduna.

Zaman sasanta rikicin kungiyar kwadago ta NLC da gwamnatin jihar Kaduna
Zaman sasanta rikicin kungiyar kwadago ta NLC da gwamnatin jihar Kaduna

An dauke wutar lantarki tare da dakatar da harkokin sufuri a daukacin lokacin yajin aikin.

El Rufai ya ayyana shugaban kungiyar kwadago ta Ayuba Wabba a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a lokacin yajin aikin bayan da ya zarge shi da laifin kassara tattalin arzikin jihar.

NLC ta shiga yajin aikin ne tana mai cewa gwamnati bai kamata ta sallami dubban ma'aikata ba.

Bangarorin biyu sun sasanta ne bayan da Ministan kwadago Chris Ngige ya shiga tsakani aka hau teburin sasantawa.

XS
SM
MD
LG