Italiya ta kai wasan karshe a gasar Euro 2020 bayan da ta lallasa Sifaniya da ci 4-2 a bugun fenariti a karawar da suka yi a Wembley.
‘Yan wasan Sifaniya sun yi yunkurin ganin sun samu gurbi a wasan karshen a kokarin da suke yi na lashe kofin a karo na uku, yayin da Italiya ke kokarin ganin ta lashe kofin a karon farko tun bayan 1968.
Bangarorin biyu sun kara har tsawon minti 90, aka kai zuwa minti 120, amma wasan ya kare da ci 1-1, abin da ya kai ga aka je ga bugun fenarti.
Yanzu Italiya za ta jira tsakanin Ingila ko Denmark wadanda za su kara a ranar Laraba a zagayen semi-final.
Masu hasashe da dama na cewa akwai yiwuwar wasan karshe ya kasance tsakanin Italiya da Ingila.
Ko da yake, wasu na ganin komai na iya faruwa, duba da yadda karawarsu ta karshe Denmark din ta lallasa Ingila.
A ranar 11 ga watan Yuli za a buga wasan karshen.
Kyaftin din Ingila Harry Kane ya nuna kwarin gwiwar cewa za su “tsallaka” a karawar da za su yi a zagayen semi-final, yana mai cewa kasar za ta kai wasan karshe a karon farko a gasar ta nahiyar turai.