Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Messi Ya Zama Dan Wasa Mai Zaman Kansa


Lionel Messi (AP)
Lionel Messi (AP)

Kwantiragin Lionel Messi a Barcelona ya kare a ranar 30 ga watan Yuni, abin da ke nufin dan wasan wanda dan asalin kasar Argentina ne na zaman kansa kenan.

Sai dai kamar yadda shafin Sky Sports ya ruwaito, shugaban kungiyar ta Barcelona Joan Laporta, ya ce yana da kwarin gwiwa Messi zai sabunta kwangilarsa da kungiyar.

“Muna so ya zauna, kuma Leo na son zama, komai na tafiya daidai.” In ji Laporta.

Euro miliyan 500 Barcelona ta biya Messi kan kwantiragin shekara hudu, wanda ya kare a ranar daya ga watan Yuli.

Messi dan shekara 34, ya kwashe daukacin rayuwarsa ta kwallo ne a kungiyar ta Barcelona.

Ko da yake, ya yi yunkurin kungiyar a kakar wasa ta shekarar 2019-20, bayan da ya nuna cewa ba ya jin dadin inda kungiyar ta dosa.

Amma daga baya an ga ya ci gaba da zama.

Akwai manyan kungiyoyi da suka nuna sha’awar sayen dan wasan, amma rahotanni na cewa wakilansa da hukumomin kungiyar ta Barcelona suna kan tattaunawa kan wani sabon kwantiragi.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG