“Ziyarar ta kunshi fitowa karara mu fada musu cewa matakin da suka dauka zai shafi alakarmu da taimakon da muke ba su ta fuskar tattalin arziki, wanda ba mu da zabi illa mu janye su bisa tsarin doka, idan har ba a maido da tsarin dimokradiyya ba.” In ji Nuland.
A cewar Outtara, tura dakarun ECOWAS ba bakon abu ba ne, yana mai cewa, a baya an tura su kasashen Liberia, Saliyo, Gambia da Guinea Bissau.
Wasu kasashe musamman a Afirka, kungiyoyi, malamai da shugabannin gargajiya da jama’a da dama sun nuna a yi taka-tsantsan kan daukar matakin na soji.
“Na farko dai ba mu santa sosai ba, ba mu ma santa ba, to tun da ko ba mu santa ba, ai kun ga ba mu da ma’auni da za mu ce za ta iya wannan aiki ko ba za ta iya wannan aiki ba.” In ji Ganduje.
A ranar Asabar za a bude zagayen da karawa tsakanin Switzerland da Spain, sai karawa ta biyu tsakanin Japan da Norway.
Sannan tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana a gaban wata kotu a Washington D.C., inda aka tuhume shi da laifin yunkurin sauya sakamakon zaben 2020.
A ranar Laraba, Tinubu ya aike da jerin sunaye 19 a karo na biyu, ciki har da sunan Shetty.
“Ina kira ga Amurka da daukacin kasashen duniya, su taimaka wajen maido da doka da oda a Nijar." Bazoum ya ce cikin makalar da ya rubuta.
Janar Abdulsalami Abubakar ya ce tawagar za ta je Nijar ta gana da shugabannin da suka yi juyin mulki su kuma mika musu bukatun kungiyar Kungiyar ECOWAS.
A tsakiyar watan Yulin da ya gabata tsohon shugaban jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya yi murabus daga mukaminsa.
Gangamin har ila yau na zuwa ne yayin da kasar ta Nijar take cika shekaru 63 da samun ‘yancin kai daga Faransa.
Wannan adadi ya kai jimullar sunayen da Tinubu ya aikawa majalisar zuwa 47 yayin da sabuwar gwamnatin ta doshi wata uku da karbar mulki.
“Tun jiya (Talata) Najeriya ta katse babbar hanyar layin da take samar wa Nijar wuta.” Wata majiya a kamfanin wutar lantarki na Nigelec ta fadawa AFP.
Ganawar ta Blinken da Bazoum na zuwa ne yayin da sojojin da suka yi juyin mulki suka nada gwamnoni a jihohi takwas da ke kasar.
Zanga-zangar ta adawa ce da tsare-tsaren gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wadanda kungiyoyin suka ce sun jefa al'umar kasar cikin kangin rayuwa.
Ita dai Ingila ta lashe wasannin uku a jere ba tare da ta shan kaye ba, yayin da ita kuma Najeriya ta yi canjaras sau biyu ta kuma shammaci Australia da ci 3-2.
Tinubu ya kuma jinjinawa kamfanoni da ma’aikatu masu zaman kansu da suka riga suka yi karin albashi.
Sai dai sanarwar ba ta ambaci takamaiman dalilin da ya sa shugaban wanda ya karbi mulki a watan Mayu zai yi jawabin ba.
A ranar Laraba 26 ga watan Yuli, sojojin da ke tsaron lafiyar shugaban Nijar Mohamed Bazoum suka kaddamar da shirin karbe ragamar mulkin kasar.
Domin Kari