Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce batun daukan matakin soji a kokarin da kungiyar ECOWAS ke yi na shawo kan rikicin Nijar na nan.
Sai dai Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar ta ECOWAS, ya ce sun fi so a bi hanyar lumana wajen sasanta rikicin.
“Za ku lura cewa daga wannan matsayar karshe da aka fitar a taron, ba mu cire kowane zabi daga irin matakan da muke fatan dauka ba, ciki har da batun daukan matakin soji a matsayin mataki na karshe.
“Idan ba mu yi da kanmu ba, babu wanda zai yi mana.” Tinubu ya ce yayin jawabin nasa.
Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a jawabin karshen taron da mambobin kungiyar suka yi a Abuja a ranar Alhamis.
Taron gaggawan da kungiyar ta kira, na zuwa ne kasa da mako guda bayan cikar wa’adin da ta ba sojojin Nijar kan su maido da tsarin mulkin dimokradiyya tare da sakin Shugaba Mohamed Bazoum ko kuma a dauki matakin soji a kansu.
Wa’adin dai ya cika tun ranar Lahadi kuma sojojin sun ki mika wuya.
Wasu kasashe musamman a Afirka, kungiyoyi, malamai da shugabannin gargajiya da jama’a da dama sun nuna a yi taka-tsan-tsan kan daukar matakin na soji.
A ranar 26 ga watan Yuli, sojojin da ke tsaron fadar shugaban Nijar suka hambarar da gwamnatin Shugaba Bazoum.
Dandalin Mu Tattauna