Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya cire sunan Dr. Maryam Shetty daga jerin sunayen mutanen da ya zaba a matsayin minitoci.
Wata wasika da shugaban ya turawa Majalisar Dattawa, ta nuna cewa an cire sunan Dr. Maryam Shetty daga Kano an kuma maye gurbinta da Dr. Mariya Mairiga Mahmud.
A ranar Laraba, Tinubu ya aike da jerin sunaye 19 a karo na biyu, ciki har da sunan Shetty.
A baya ya tura sunaye 28 ga majalisar.
Kazalika Tinubu ya kara sunan tsohon karamin ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo, a sauyin da ya yi wa jerin sunayen da ya aika a karo na biyu.
Shugaban Majalisar Dattawan Godswill Akpabio ne ya karanto wadannan sauye-sauye a zauren majalisar a ranar Juma’a, yayin da ake ci gaba da tantance mutanen da aka zaba.
Dandalin Mu Tattauna