Shi dai Obi a birnin Jos ya girma, kuma ya fara wasan kwallonsa ne a garin inda daga baya ya shahara.
Blinken ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da ya yi da Bazoum ta wayar tarho a ranar Laraba.
Kungiyar ECOWAS da AU da Majalisar Dinkin Duniya sun yi kira da a saki Bazoum cikin gaggawa ba tare da gindaya wasu sharudda ba.
Yan Najeriya sun jima suna dakon fitar da jerin sunayen ministocin yayin da wa’adin da doka ta tanada na mika sunayen ya zo karshe.
Wannan mataki ya biyo bayan ziyarar da Shugaba Talon ya kai wa Tinubu a fadarsa da ke Abuja a ranar Laraba.
Cikin wata sanarwa da ECOWAS ta fitar a ranar Laraba, kungiyar ta yi kira ga dakarun da ke da hannu a yunkurin juyin mulki da su hanzarta sakin shugaban kasar saboda an zabe shi ne bisa tsarin mulkin dimokradiyya.
“Bayanai na nuni da cewa Shugaba Mohamed Bazoum na hannun dogarawan fadarsa." In ji wakilin Muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.
Hatsaniyar ta kaure ne a lokacin da jami’an gidan yari da na hukumar farin kaya ta DSS suka fara kai ruwa rana kan wanda zai tafi da Emefiele bayan da aka kammala zaman kotun.
“Ina mai matukar farin cikin fara wannan tafiya da abin kaunata …. Mata da miji na nan tafe.” In ji Bishara.
Tuni dai Davido ya cire bidiyon a shafukansa na sada zumunta bayan da aka yi ta sukar shi a dandalin yanar gizo.
Daga cikin wadanda suka bayyana aniyarsu a baya-bayan nan, akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Mike Pence da tsohon Gwamnan jihar New Jersey Chris Christie.
A ranar 29 ga watan Mayu za a rantsar da zababben Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima.
Kafin nada ta a wannan mukami, Oluwatoyin ta kasance Darektar Kudi a Ofishin Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya.
"A yau na zagaya da uwargidan zababben shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu fadar shugaban kasa don ta ga zubin fadar." In ji Aisha.
Sakatariyar Baitul Malin Amurka, Janet Yellen, ta yi gargadin cewa idan har ba a fadada damar karbar bashin ba, nan da farkon watan Yuni gwamnati za ta rasa kudaden da za ta kashe.
Hukumar NIDCOM da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare ta ce da misalin karfe 3:15 na yamma jirgin kamfanin Tarco mai lamba B737-300 ya sauka a Abuja.
Domin Kari